Connect with us

KASUWANCI

Manoman Borno 2,000 Sun Koma Yobe – NECAS

Published

on

Shugaban kungiyar NECAS ta Kasa da ke a yankin Arewa maso Gabas, Alhaji Sadik Umar Jaware, ya sanar da cewa, kimanin  manoma su 2000 ‘yan asalin Jihar Borno suka koma Jihar Yobe don suci gaba da yin sana’ar ta su ta noma.

Alhaji Sadik Umar Jaware ne ya sanar da hakan ne a lokacin haka kaddamar da raba taraktocin noma guda dari  ga wasu  manoma da aka zabo daga cikin kanan hukumomin 17  na jihar. Shugaban ya ci gaba da cewa, tagomashin da akayiwa manoman an yi shi ne da nufin tallafawa  manoman da aka raba da muhallansu, damar noma a gonakin Jihar Yobe, don samun dogaro da kai, tare da wadatar cimaka a yankin.

Alhaji Sadik Umar Jaware  ya kuma koka a kan yadda moman suka bar jihar, inda Shugaban ya kara da cewa,  kafa kungiyar ce da nufin habaka noman zamani a yankin. A cewar sa, za a cigaba da rabar da taraktocin noma 600, a daukacin yankin. Shugaban ya yi nuni da cewa, bisa la’akari da bukatar da Jihar Yobe ke da shi ga kungiyar, an kaddamar da raba taraktocin guda dari  a jihar, don inganta noman zamani.

Da ya ke kaddamar da raba taraktocin, Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, ya shawarci manoman su rungumi noman zamanin da nufin tada komadar tattalin arzikin jihar, wanda ta’addacin Boko Haram ya gurgunta.

Ya yi nuni da cewa, babu wata kasa a fadin duniya da zata iya yin ikirarin kula da alummar ta in ba ta hanyar noma ba. A karshe Shugaban kungiyar ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin Jihar a shirye take ta kulla hadaka da  sauran kungiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu don kara bunkasa noma a jihar.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: