Connect with us

Uncategorized

An Kama Dan Sandan Bogi Da Motar Sata A Anambra

Published

on

An kama wani dan sandan bogi mai suna Hassan Abuka a garin Anambra tare da wata mota kirar Toyota Corolla wadda ake zargin an satota ne daga Legas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Anambra SP Haruna Mohammed, ne ya bayyana haka ga manema labarai, wanda ya ce, wanda ake zargin mai kimanin shekara 33 dan asalin jihar Benuwe ta hanyar amfani da fasahar zamani ta bin sawu.

Haruna ya ce, “ Da misalign karfe 4:30 ny, bayan da muka samu labara, rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaki da ‘yan fashi sunkama Hassan Abuka a Ihiala, sanye da ciakken kayan ‘yan sanda mai mukamin DSP tare da wani Isma’ila Ahmed mai kimanain shekara 37  dan asalin garin Otukpo, ta jihar Benuwe.

“Wadanda ake zargin sun kware wajen yin amfani da kayan ‘yan sanda domin cutar mutane. An kama su da mota kirar Toyota Corolla mai lamba AGL 357 FC, wadda kuma har zuwa lokacin hada wannan labarin ba a gano mai ita ba. An kama wadanda ake zargin da mota da kuma wata lambar mota FKJ 701 FR.”

Haruna ya ce. Sun amfa zargin da ake yi musu, kuma suna ci gaba da bai wa ‘yan sanda bayanai kan binciken da ake yi musu, wanda bayan gamawa za kai su kotu domin fuskantar hukuncin da ya dace.

tarwa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: