Connect with us

LABARAI

An Shiryawa Marayu Fiye Da 500 Walima A Zariya

Published

on

Ranar Larabar da ta gabata ne kungiyar daidaita aure da tallafawa marayu da marasa karfi da aka fi sani da INA MFITA FORUM wadda cibiyar ta ke Zariya, ta jagoranci yin walima ga wasu marayu maza da mata a Kwalejin ilimi na gwamnatin tarayya da ke Zariya.

Taron walimar da kungiyar ta shirya, a cewar shugaban kungiyar,  Malam Bashir Abubakar Magaji Basharata, sun saba a duk shekara su zauna da marayun da suke karkashin kungiyar da Sallah, domin raba musu tufafin sallah, in kuma lokacin bukukuwan sallah ya yi, suna zama da marayun kujera daya akushi daya, su ci abinci tare da su, tare cin naman layyar dabbobin da aka yanka dominsu.

Wannan taro da suke yi a duk bayan sallah, kamar yadda ya ce, sun a debe wa marayun ne yunanin yadda su ke zama tare mahaifinsu a lokutan sallah da kuma yadda mahaifinsu ke samar musu da abinci da abin sha da kuma tufafi a lokutan Sallah, shi ya sa wannan kungiya ke tsara taron walima domin marayun, in ji Malam Basharata.

A wannan shekara ta 2019 da ya yi daidai da 1440, kungiyar ta yi wa marayu fiye da 400 kayan sallah, tun daga riguna da wanduna da zannuwa da hijabai da takalma da kuma sauran kayayyakin kwalliya da mace ke bukata, duk wannan kungiya ta tanada, ta kuma raba wa marayun da suke karkashinta.

A kuma game da daidaita aure da aka kafa kungiyar dominsa, Malamin ya ce, sun daidaita aure guda 170 a sassan karamar hukumar Zariya da wasu kananan hukumomi da suke ciki da wajen jihar Kaduna,

kuma wannan kungiyar, kamar yadda shugaban kungiyar ya ce, sun hada aure guda biyar a karkashin wannan kungiya ta INA MAFITA FORUM da nan Zariya.

Malam Basharata ya kara da cewar, su kan su marayun da kuma iyayen marayun mata, wannan kungiya ta samar ma su da sana’o’in dogaro da kai, maimakon jiran tallafin kungiyar daga lokaci  zuwa  lokaci, wannan ya sa, in ji Malam, marayu da kuma iyayen marayun mata, sun sami hanyoyin da suke dogara da kan su, mai makon jirar tallafi daga wannan kungiya.

A dai jawabinsa ya nuna matukar jin dadinsa ga Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris na tallafin day a ke yi wa wannan kungiya da kuma yadda a kwanakin baya ya bayar da babban Sa, ya ce a yanka wa marayun da Sallah, da  Uwar marayu ta wannan kungiya, Hajiya Amina Jafar na yadda ta ke bakin kokarin tan a bayar da tallafi na kudi da tufafi da kuma abinci ga marayun da suke wannan kungiyar sai kuma Chiroman Shantalin Zazzau, da shi ma ya ba da  rago ga wannan Kungiyar, domin a yanka wa marayu.

A karshen jawabinsa Malam Basharata, ya ce a kwai wani tsari da su ke yi ga ‘yan mata da suka isa aure, inda su ke koya masu dabarun yadda za su zauna da miji da kuma yadda za su yi kwalliya a gidajen mazansu da dai sauran hidimu da ya dace mata su sani kafin yin aure.

Shi ma jawabinsa Chiromann Shantalin Zazzau Alhaji Abubakar Ladan, ya yaba wa shugabannin wannan kungiyar da kuma yin alkawarin ci gaba da tunanin hanyoyin da zai bi tare da shugabannin kungiyar ta yadda marayun za su sami damar ci gaba da karatunsu a ko wane mataki na ilimi ta daukar nauyinsu.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen taron walimar sun hada da Hajiya Amina da kuma Khalifa Abbas Sama’ila Abbas Dakace da dukkansu, suka yaba wa shugabannan wannan kungiyar da kuma kira ga al’umma da su kawo wa wannan kungiyar gudummuwar da duk abubuwan da suka dace, domin su samu damar kula da marayun da suke karkashinsu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: