Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (56)

Published

on

Hamdiyatul’aini Ta Karya Daular Aswadu Dan Sauda’u

An yi tsawa a tsakiyar Anhaarussalasa, wadansu koramai masu gudana gami da ingizar juna. An jiyo wata sanarwa daga sautin mace mai magana da harshen Ibraaniyanci, daura da wata katafariyar alkarya mai makotaka da wani tsauni inda fadar wani bakin Shaidani Abu Jurmuuza take, wadda daga can ne boka Nammamu ke karbar soko domin isar da shi ga sarki Aswadu dan Sauda’u.

Mazowa alkaryar daga sashen fatake sun ga wadansu irin halittu daga nau’in tsuntsaye suna baro shiyyar Gabas suna ta komawa Yamma, daga baya tsaunin ya yi bindiga a yayin tsawa ta biyu, al’amarin da ya alamta musu lallai wani tashin hankali na tafe.

Sashen al’ummar alkaryar yana yi wa sashe tambihi kan yiwuwar ci gaba da zama cikin wannan yanayi. Daga karshe sun ga wasu jama’u na mutanen da ba mutane suna tasowa daga saman wani dutse kamar dai cewa su suna gudun hijira ne don gujewa faruwa wannan lamari.

Hamdiyatul’aini ta yi sansani ita da sauran jama’arta a bayan gari a sanyin safiyar suka sauka a wannan gari bayan sun tsallake wancananka kogi. “ Wa zai iya shiga cikin garin nan a cikinku ya gano min yadda al’amura suke,” ta fada tana mai tambayar su. Kowa ya yi shiru, ta dube su ta ga duk kamar ma a hayyacinsu suke ba, saboda razani. Ana cikin wannan hali sai ga wadansu samari nan su shida suna tafiya bisa dawaki.

Da suka hango su sai kuwa suka sakarwa dawakinsu linzami suka same su, “ Kai wadan nan jama’u daga wata alkarya kuke, yalla ku baki ne ko, hala ma dai baku da masaniyar wannan alkarya?” sai daya daga mutanenta ya kalle ta sai ta yi masa izni da amsa musu. “ Haka ne mu baki ne hanya ce ta biyo da mu, shi ne a yanzu muke tunanin ta yaya za a yi mu shiga wannan alkarya gudun kada mu bi hanyar da ba a bi mu karya muku doka,” in ji shi.

“ To mu dai da kuke ganinmu masu lura shige da fice ne, amma kun taho fatauc ne ko kuwa, idan dai fatauci kuka fito, to gara ku koma ku tsallake kogin nan, idan kun yi tafiya ta kamar yini biyu za ku samu wata alkaya da wata yarinya ke mulkarsu, a nan za ku samu rayuwa mai inganci, amma na kasar duk wanda ya shiga baya fita, kuma mulki ake yin a zalunci. Yanzu waye jagoran tafiyar taku?” in ji daya daga cikin fadawan sarki.

Sai suka yi ishara ga Hamdiyatul’aini, suka duba suka ga fuskar yarinta. “ Kash amma dai ku an yi wasu tashin kauye, ta yaya za ku shugabantar da dan karamin yaro a samanku, yalla ko da dan sarkin garinku ne?” a’a haka nan muka tsara don kanmu domin mun gay a fi mu ilimin addini, shi ne muke ganin zai fi mu hangen nesa.” In ji daya daga mutanenta.

Bafade ya yi dariya ya ce, kai amma dai ku an yi sakarkaru, to yanzu idan a ce ‘yan fashi ne suka tare ku fa wannan dan karamin yaro da ko magana bay a iya yi shi ne zai tare muku”? in ji bafade.

Daya daga cikin mutanenta ya ce, ai ba mu nada shi ya tare mana fad aba, bari dai yana matsayin wanda zai rika sa mu a hanyar mai haske cikin ilimin addini.” “ Kai ka dube su wai har addini suke da shi, ai mu nan sai dai in mun zauna mu ba da tarihin da muna Sallah amma ba yanzu ba. idan fa kuka sake wasu irinmu suka zo to fa su ba za su tsaya yin hira da ku ba, daga nan ne mu ma za mu juya muku baya, gara ma tun da wuri ku kama hanya.” In ji fadawan sarki.

Daya daga cikin mutanenta ya ce, ai idan ka ga mun motsa daga nan mun samu umarni daga Shugaba.” Sai daga cikin fadawan ya harare shi ya ce ku zo mu tafi, ga dukkan alamu hankali bai ratsa jikinsu ba. Har sun juya sun fara tafiya sai daya daga cikin jama’ar sarauniya ya ce, samari to taimaka ku kai mu ga sarkinku mana. Babban su ya juyo a fusace ya zo gabansu ya tsaya y ace, kai mahaukaci ne, a she baku da hankali? Idan muka shiga da ku mutuwa za ku yi, don haka za mu tafi idan ma mun ga wasu ba za mu bari su zo nan ba, saboda mun ga ku musulmi ne, daga nan ya juya ya bi ‘yan uwansa.

Bayan sun dan yi nisa saraniya ta ce,  “Jassasa ta yi gaskiya, amma mu bari su shiga cikin gari daga baya sai mu tasamma gidan sarkin.” Haka kuwa aka yi bayan sun daina hango su sai suka bi su a baya har suka kai ga kofar gari, suka samu masu tsaro suka tambaye su ko ina za su bi zuwa gidan sarki? Ma su tsaro su dube su ku kuma daga ina?

A nan sarauniya ta yi magan cewa, “ Kai mun gaji da amsa tambayoyi marasa fa’ida, in kuna iyawa ku nuna mana hanyar da za shiryar da mu zuwa gidan sarki.” Masu tsaro ba su gardama ba suka nuna musu hanya, “ Ai wanda bai ji bari ba ya ji hoho.” Ta juyo ta ce, “ Ai mu mun ji bari don haka sarkinku ne mai jin hoho a yau.” Ta juya suka ci gaba da tafiya, ba sujima da fara tafiya ba, sai ta hango bakin hayaki na tashi daga wani wuri kamar lambu, ta kada limzamin dokinta ta nufin wurin. daya daga cikin masu tsaron nan ya rugo da gudu ya tari gaban dokinta, “ Don Allah ‘yata kada ki bi wannan hanyar ba ta biyuwa haryar gidan boka ce duk wanda ya bi baya dawowa, kuma ke ga ki mace ma kamar ‘yar sarki.

Ya kalli sauran jama’arta cikin fushi ya ce, ku wadanne irin sakarkaru ne za ku taho da wannan yarinya haka, ba ku da labarin wannan alkaryar ne.?” daya daga cikinsu ya ce, “ Eh, muna labari, amma yaya za mu yi da umarnin uwargujiyarmu?” ya kuma cewa “ ‘Yata na roke ki da ki koma ki bi wata hanyar. Ta ce, “ Baba sai dai ka yi hakuri domin na rantse sai na je na ga abin da yake fitar da hayaki a can wurin.”

Ya ce, babu komai a ciki sai hallaka, gidan hamshakin boka ne wanda duniyar mutane ta jima ba ta samu irinsa ba.” Ta ce, yawwa ka ga kuwa ban taba ganin yadda ake sihiri ba yanzu kam zan je na gane wa idanuna, ku ku jira ni zan zo maku da labari in sha Allahu, daga nan ta kada linzaminta ta ci gaba da tunkara lambun. Bafaden nan ya kalle su ya ce, to ku yi maza ku koma kasarku kafin masu kama baki su zo, ku gaya wa sarkinku ‘yarsa ta hallaka.

Suka ce za mu zauna nan har sai ta dawo idan da hali, ba za mu iya tafiya babu ita ba. “ To har abada ba za ta dawo ba ta hallaka kenan.” Ya juya ya basu wuri, suka ci gaba da jiran ta.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: