Connect with us

HANGEN NESA

Auren Mace Daya Lalaci, Asara Ne (2)

Published

on

Wannan ci gaba ne daga makalarmu ta makon jiya dangane da auren mace fiye da daya.

Ga shi kuma kafircinmu (idan na ce kafirci ina nufin Musulmi amma mai hali iri na kafirci ne, akwai da yawa a yau) na riko da mata daya ba zai bar mu auren ta biyu, ta uku, ko ta hudu, duk da arzikin da Allah ya ba mu. Wani albashinsa zai rike mata hudu, wani uku, wani biyu, wani daya.

Kowa daidai yadda ya dauki rayuwar. To, amma wanda Allah ya ba shi albashin rike mata hudun ma ba zai yi ba, ba zai iya yi ba domin kafirai (‘yan uwa musulmi da suke daura wa karya da barna gindi, wadanda suka dauko rayuwar Yahudawa suka kakaba wa kawukansu) da suke tare da mu ba za su yarda ba. Sau da yawa idan mai niyya ya dauri niyyan karin aure sai ka ga kafirai su yi duk abin yi wajen tabbatar da auren bai iyu ba.

Akwai wani mutum ya dau abokinsa da ya aminta da shi, ya kaishi wani gari wajen ganin iyayen yarinya da zai aura, kari na biyu. Daga dawowarsu, sai abokin ya nemi matar (abokin nasa) mai niyyan kara auren ya gaya mata dukkan labarin shirin mijinta na kara aure.

Kafin ka ce meye, sai ga matar ta shiga fitina da yarinyar sai rikici sai tashin hankali. Tun ba a yi auren ba da matar da yarinyar duka suka dau tashin hankali tun kafin a yi auren. To, yaya zata kasance ne idan an yi auren? Sai ta Allah kawaii!.

Sai kuma wanda yana neman aure na biyu domin Allah, domin cikita addininsa, har Umara ya je rokon Allah mata ta gari, sai ga labarin wata baiwar Allah Bazawara, Mijinta ya rasu shekara bakwai ke nan, yaranta mata biyu, suna makaranta.

Sai mai niyyan aurenta ya ce, “Alhamdulillah, faduwa ta zo daidai da zama, shi kenan ma abin nema ya samu, sai in rike yaran na tarbiyantar da su, na sanyasu a makaranta na sami ladansu,”

Sai ya shiga nemarta, amma da farko mata na gardama, gaskiyarta, aure ba wasa, sai an bincika, abu dai ya kusan rushewa, wai wani dan babban Malami yana sonta, wai Babanshi ne ya nema mashi. Sai bawan Allah talaka ya ja ya hakura.

Kamar da gaske sai ga labari ya iso cewa yaron Malam ya riga yayi aure, sai an ce talaka ya dawo, an biya sadaki an daura aure. Shekara da rabi shiru. Ango ya kama gida mai daki uku a inda yake, shekara ta wuce ya kara biya.

Da an ga tare wa ya gagara kuma ba bayani, dangin miji sun je gidansu amaryan sun ce idan wannan tarewar ba zai iyu ba, a fasa auren. aka mayar da rabin sadakin. “Sauran rabin ku dawo ku karba idan ta sami miji”.

Shekaru hudu bayan nan, har yanzu tana nan, ba aure, ba mutunci, shi ma mijin ya fasa auren domin shi don Allah yake son auren, amma mata kuma basa don Allah. Hasali ma wai ashe sun dauka yana da kudi ne, ashe babu. Duk rayuwarmu ta zama kudi, komai kudi. Har Kur’ani da hadisai mun yi musu farashi, ga shi kuwa muna shan azaban tun anan.

Sau da yawa na kan ji samari ke cewa: sai na yi kudi zan yi aure; wannan mai tunanin mai iyuwa ya gama makaranta ke nan, ya sami digri na farko. Mu kaiyada shekarunsa ashirin alal-akal ma kenan. Mai iyuwa ya kara shekaru biyar kafin aikin ko kudi ya zo sa’annan yayi aure. Bai san shekarunsa na jaa ba. Sa’annan baya aiki da kira da muke yi cewa mata da yawa suna zube ba aure. Idan kai ka noke, wa zai auresu.

Shi aure baya yiwuwa a halin yanzu idan ba kudi. Dole ne a sami mahalli da tabarma da za akwan akai. Dole ne a nemi abinci, dole ne a nemi magani idan jinya ta zo. Kudi yanan da amfani. Amma duk kudin da muke alakanta wa aure ba irin kudin biyan bukatun ma’aurata kawai ba ne. Kudin dogon buri muke nufi, shi kuma wannan arziki ne daga gun Allah, idan da rabo zaku samu.

Amma kuma idan satan kudin al’umma ake nufi to kuma sai mu ce Allah ya sawwaka, domin sata da wuya kuma anan gaba kadan. Sa’annan Allawadaran wanda yana jiran hanyan sata sa’annan yayi aure. Idan Allah ya nufeka da alkhairi kam ma ba kai ba aure idan sai ka saci kudin al’umma ne.

Duk baki da Allah ya bude zai ci abinci, sabida haka babu bukatar jiran aiki kafin aure. Muddin ka yi karatu ai ka gama komai, abinci kam zaku ci, kuma rufin asirin ba arziki ke kawowa ba. Allah ne mai rufa asiri.

Don haka a yi aure da zaran an gama makaranta, dadin hakan shine zaku girma da yaranku, har ma ka ji idan sun girma an a ce maka “ko kaninka/ki ne wannan” yana da dadi, shi ya sa iyayenmu sun cika aure da wuri.

Kuma mu sani, muddin mun allaka aure da kudi kuma kudin ba zai zo ba, sai dai kuma koma baya, na ga samari da yawa, na ga ma’aurata da yawa suna jiran kudi kafin su yi aure ko su kara.

Ga shi har yanzu suna can suna jira, ba kudin kuma ba aure, idan an lallaba an yi aure arzikin ku guda biyu zai koro aiki da kudi da wuri. Idan kuma an jinkirta to sai a shirya wa irgen shekaru ba a yi ba. Shi ga yawan tunani, sai shiga shaye-shaye, muggan kalamai, wata kila ma har sabo ba a yi istikfari ko jaddada salati ba.

Ba tulin kudi ne ke sanya karin aure wanzuwa ba, kyakkyawar niyya da tsari wa iyali na taimakawa matuka wajen karfafan zamantakewar aure, kari kan hakan adalci.

Wancan irin tunanin yafi yawa a arewacin kasar nan, buri yayi mana yawa, komai muke don birge mutane muke yi, shi ya sa mun ce a baya ba mu cika yin abu don Allah ba sai don riya, shi ya sa yawancin aurarruka da aka yi sukan rushe jim kadan bayan nada su. Babu Albarka, babu rahamar Allah da yardarsa a ciki, a kashe kudi da yawa wajen sabon Allah a lokutan biki, a lokancin ne duk albarkan aure takan salwanta ba mu sani ba.

Iyaye da malamai ba su taimaki al’umma ta wajen tashi tsaye wajen horar ‘ya’yansu wajen kula da tafarkin aure tun daga farko, daga wajen nema har tarewa, a tsakanin nan akwai dogon lokaci.

Akan samu matsaloli da illoli da yawa, Akan sami sabanni da yawa a tsakanin ma’aurata, shi ya sa jan lokacin nema babu amfani, daga zaran an hadu, an fahimci juna, sai a yi sauri a nada, Allah kuma zai sa Albarka a ciki.

Ina da misalai da yawa inda aka yi amfani da wannan shawartawa kuma an ga amfani, ba mu cika gani ko fadin amfanin kyawun rayuwa idan ta inganta, sai yawan korafi kawai muke na matsaloli.

Ba mu cika ganin amfanin rayuwa idan tabi tafarkin Allah, magabata da iyaye ba, ba mu cika gode wa Allah kan ni’imomi da ya kanyi mana ba, mun zubar da komai.

A lokuta da yawa, mu kanmu ne mukan zama musabbabin auren da muke yawan son mu yi, Mu kan yawan shimfida gabatarwarmu ga mace akan karya da karya, Ba mu da shi mu ce muna da, Kodayake wannan ya ta’allaka ne akan wata tsohuwar magana da ke cewa: ana auren mata da karya sai a rike su da gaskiya.

Amma ba a zamanin yanzu ba, hakan ya kan isa yaudara ce ma, a yi ta Gar, wai sunan wata gari a kasar jihar Bauci ta gabashin birnin Baucin. Wani lokaci har idan matar ta zo gida ma karyar takan ci gaba, duk inda aka boye gaskiya sai ta tsiro, sabida haka ba karya ba yaudara. Idan za a yi a yi, idan ba za a yi ba kuma kowa yayi gabansa.

Dubi irin wulakanta aure da muke yi, sannan mu dawo muna kuka wai kannenmu, antinninmu, da yaranmu basa aure domin ba mu ji, Allah Sarki! Allah ya bayar amma wasu sun hana, asshe ba auren ne ba, kudi ne, Allah mai hakuri, sannan su kansu matan ba su san abinda ke damunsu ba.

Wallahi a koma ga Allah, irin wannan kira tawa da kalamai na na wa’azi abin wasa ne a yau a wajen mutane da yawa, amma kuma babu makawa, daga gaskiya sai bata, har na rasa abokai, na rasa matar aure domin abinda nake fada a rubutuna.

Kuma komeye zan kara rasa bazan daina maganar da tafi maslaha ga al’ummar arewa da kasar nan. Bazan fasa fadin abinda muka ga illa ne ga jama’a ba. Ina kuma rokon Allah yasa na mutu da mata daya idan ba auren saboda Allah ba.

Wallahi aure kam tuni ta zama aikin gayya ne ko aikin agaji na al’umma, duk wanda ya daura niyan aure ko kari a yau ya debi babban taimako ma arewa. Kuma ladan wannan auren Allah kadai ke da saninsa, domin haka, ‘yan uwa na maza mu yunkura don Allah don Annabi.

Mu tashi mu yi auren don Allah domin Allah, sai Allah ya tallafa mana wajen budin arziki da rikon auren cikin lumana da aminci, a irin halinmu na yau da fitinar mata ta yi yawa, duk wanda yana da hali sannan ya rike mata daya wai, “my sweetheart I lobe you”, ya shirya gamuwa da Allah tun duniya.

Wallahi ba wasa, wannan shi ne karshen zamani da muke fadin labari. To, amma meye aka ce mu yi idan muka sami kanmu a ciki? Ka gani? Hallin mushkila kawai mu rage son kai mu taimaka, sai dai idan yana da dalilai kamar nawa, wato an washeshi don ra’ayinsa na la’akari da Allah sai gaskiya ko kuma ya sha nema yana faduwa ba nauyi.

Idan ba ko daya to wallahi da gyara, shi ya sa kuna ga munashan wuya, son kudi bai bamu kudin ba kuma mun sake hanyar Allah, sai wahala, Duk wanda yana da hali amma zauna da mata daya, ya jawo ma kansa wahala, ba zai rabu da talauci ba, sannan duk abinda ya sa hannu a ciki ba zai yi albarka ba.

Allah ya sakawa wadanda suka yi yunkurin aure sau da yawa ba su dace ba. Inshaa Allahu akwai gaba, ba fashi, a ci gaba da nema. Sai dai wani mai gidana ya ce idan ka yi ka yi karasa sai ka tsaya nan, Rabonka zata zo nan ta sameka, ban san sahihancin wannan hikimar ba. Amma nasan maganar manya bata fadi a banza, Allah ya kawo na gari.

Kuna iya rubuto mana akan batutuwan da sharhinmu ke jawo da kuma ra’ayinku akan matsalolinmu na arewa, musamman ma wadanda suke ta kasa, Mu lura a kasa. Illolinmu suna nan a kasa, a tsakaninmu. Mun cika hangen shugabanni mu bar namu illolin.

Kuma duk inda ka fara korafi akan wani abu, to ka dubi kanka, kai yaya kake? Kana cikin yawaita matsalar ko kana wajen ya kanta? A kullum kada mumanta da hakan. Hakan ne kawai zamu iya fadada canji da muke bukata.

Allah ya sa mu gyara, sai wani makon, idan Allah ya kaimu. Nagode, a aiko mana dukkanin sako kai tsaye ta nan 08050551220.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: