Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sallah A Garin Daura

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo garin Abuja babbar birnin kasar nan bayan da ya yi hutun babbar sallah a mahaifarsa dake Daura ta jihar Katsina.

Shugaban kasan ya tashi ne daga filin saukan jiragen sama na Umaru Musa Yar’Adua dake Katsina da misalign karfe 11 na safen jiya Asabar zuwa Abuja.

A yayin zamansa na hutun a garin Daura, Shugaba Buhari ya kardi bakoncin manyan mutane da dama daga ciki da wajen kasar nan ciki har da shugaban kasar Guinean, Alpha Conde da shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan  da mataimakinsa, Odie OmoAgege; da wasu gwamnonin tarayyar Nijeriya 12.

Haka kuma shugaba Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya da jaje ga wadanda harkokin ta’addanci ya rutsa dasu a wasu kananan hukumomn jihar Katsina, musammam dai ya sadu da al’ummar karamar Batsari, haka kuma ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar Katsina ta gudanar da kuma babban asibitin sojojin sama a garin Daura.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: