Connect with us

Uncategorized

Burinmu Mu Fara Yin Kayan Sana’o’i Irin Na Kasar Waje – A’isha Gambo

Published

on

Shugabar gamayyar kungiyoyin mata masu yin kayan sana’o’in hannun wato a Turance. “Women Skills Iniatibe” Hajiya A’isha Gambo ta sanar da cewa, burin kungiyarsu shi ne, su fara yin kaya kamar irin na kasashen waje.

A’isha ta sanar da hakan ne a  hirarta da Jaridar wakilinmu a Kaduna, lokacin da kungiyar ta yi bikin baje kolin kayan sana’oin hannu da ‘ya’yan kungiyar suka yi don sayarwa a jihar da kuma kai wa sauran jihohin kasar nan don sayarwa a makarantar mata.

Shugabar ta ce, a wannan karo na biyu na baje kolin, kimanin mata masu sana’oin hannu su dari ne suka baje kayan sana’oin hannu da suka yi da kansu.

A cewarta, “Mun samu ci gaba daga lokacin da muka gudanar da bikin baje kolin a karon farko a cikin jihar nan, domin kuwa, mata da dama daga wancan lokacin zuwa yanzu, sun kara rungumar yin sana’oin hannu a jihar nan.”

Ta ci gaba da cewa, “ Muna kuma da burin mu koyawa ‘ya’yanmu mata don su ma su rungumi sana’oin hannu yadda in sun yi aure za su iya taimakawa mazajensu da kuma ‘ya’yansu.”

Shugabar ta kara da cewa, “Za mu kuma kara gudanar da wani baje kolin na kayan sana’oin hannu da ‘ya’yan kungiyar suka yi a cikin watan Janairun shekara mai zuwa, musaman don fito da wasu sababbin kaya da za su yi tafiya da zamani.”

Ita ma a nata jawabin a matsayin babbar bakuwa ta musamman a  wurin baje kolin da aka gudanar a makarantar mata ta Maimuna Gwarzo, Hajiya Ramatu Mai Sarari, matar marigayi Alhaji Aamdu Chanchangi ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-rufa’i da ya taikamakawa kungiyar da  tallafi yadda matan za su samu sukunin gudanar sana’oin nasu, musamman don su zamo masu dogaro da kawunansu.

Mai Sarari ta kuma yi kira ga mata su fito su shiga cikin wannan kungiyar yadda za su zamo masu dogaro da kansu da kuma tallafawa mazan aurensu.

Shi ma a nasa jawabin a matsayin babban bako na musamman a wurin taron Sardaunan Matasan Arewa Alhaji Ibrahim Gashas ya yi nuni da cewa, ya yi nuni da cewa, idan matar aure ta rungumi sana’ar hannu babban taimako ne baki daya ga iyali da maigida, idan akayi la’akri da yadda halin rayuwa yake a yau na rashi duk iya kokarin da magidanci yake yi dakyar yake iya biyan bukatar iyalansa.

Gashas ya kara yin nuni da cewa, idan matar aure tana yin sana’ar hannu, hakan yana kawar mata da bacin rai da kuma samun aukuwar fita a tsakanin ta da mijinta.

Sai dai ya koka a kan yadda matan masu sana’oin hannu basa samun tallafi daga gun gwamnati, musamman samun sukunin a tallafa masu don samun bashi daga gun bankunan da ke tallafawa masu kanana da kuma matsakaitan sana’oi.

A karshe ya ce, akwai bukatar gwamnati, musamman gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen karfafawa matan masu sana’on hannu yadda zasu habaka sana’oin su na hannu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: