Connect with us

WASANNI

Coutinho Ya Koma Bayern Munchen A Matsayin Aro

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta amince zata bawa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen aron dan wasanta na gaba, Philliph Coutinho, na tsawon shekara daya, bayan wata tattaunawa da akayi tsakanin kungiyoyin biyu.

Tun bayan kammala kakar wasan data gabata dai aka fara danganta Coutinho da barin Barcelona sakamakon rashin tabuka abin kirki hakan yasa kungiyoyi da dama suka shiga zawarcinsa ciki har da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Itama Barcelona taso tayi amfani da dan wasan wajen cinikin Neymar inda tayiwa Paris Saint German alkawarin cewa zata bada dan wasa Coutinho da kudi domin ganin ta dauki Neymar sai dai daga baya Coutinho ya ce bazai amince da musayar ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ma taso ta dauki dan wasan dan asalin kasar Brazil amma shima yaki amincewa da komawa kasar Ingila da buga wasa wanda hakan yasa itama Tottenham, wadda taso daukar dan wasan itama ta hakura.

“Mun amince da daukar dan wasa Coutinho aro na tsawon shekara daya saboda haka yanzu mun gama kulla kowacce yarjejeniya da Barcelona akan dan wasan kuma shima ya amince zai bugawa Bayern Munchen wasa” in ji shugaban kungiyar ta Munich

Shima mai Magana da yawun Barcelona ya bayyana cewa shugabannin Bayern Munchen sun shafe kusan kwana biyu a kasar Sipaniya domin ganin sun dauki aron dan wasan kuma yanzu ta tabbata Coutinho zai koma kasar Jamus na tsawon shekara daya.

Coutinho dai ya koma Barcelona daga kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a watan Janairun shekara ta 2018 akan kudi fam miliyan 142 kuma dan wasan mai shekara 27 ya buga wasanni 76 inda ya zura kwallaye 21 tun bayan komawarsa kungiyar

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: