Connect with us

KIWON LAFIYA

Dimbin Amfanin Rogo A Jikin Dan’adam

Published

on

Rogo yana daga cikin abinci wanda ake amfani da shi na yau da kullum, yana da wasu fa’idodi masu yawa da kuma sinadarai na abinci masu gina jikin Dan’adam.

Amma babban abin da za mu yi bayani shi ne, sinadari wanda yake a cikinsa wato Bitamin (B17), wannan sinadari yana daya daga cikin abinci masu jina jikin dan’adam, kuma magani ne wanda yake hana Kamuwa da ciwan daji (Cancer), sannan yana kuma magance cutar a matakin farko idan ba ta yi tsanani ba. Haka shi ma dankali yana da irin wannan sinadarin, amma hanyar da ake amfani da shi shi ne, ana dama shi sai a sha kamar yadda ake shan wasu na’ikan abin sha. Wani kwararran likita mai suna Dakta Shuaibu ya tabbatr da wannan bincike.

Bayan haka kuma, bincike ya nuna cewa, a kan sami irin wannan na’in sinadarin a mafi yawa daga cikin ‘ya’yan itatuwa, kamar kwallon mangwaro da dai sauran su.

Gargadi

Cin danyen garin rogo kan illata lafiyar Dan’adam cikin sauri. Tabbas danyen rogo guba ce ga rayuwar Dan’adam, saboda gubar da yake dauke da ita mai suna Cyanide a turance. A kasar larabawa ba sa cin danyen rogo har sai sun shanya shi, sannan su mayar da shi garin kwaki, kafin su ci ko su kai kasuwa. Saboda babbar hanyar rage wannan guba na Cyanide ita ce, shanya garin kwaki a rana ko jika shi da ruwan zafi, shi ya sa cin teba ya fi inganci kan jika gari a ci shi haka nan. Babbar illar da garin kwaki yake wa jiki ya hada da matsalar ido, ciwon hanta, ciwon makogworo da dai sauran su. Sanin kowa ne cin danyen rogo ya sha kashe mutane har lahira, kai har ma dabbobi, saboda yanzu haka akuya ko tinkiya ta ci danyen rogo, to tabbas ba ta kwana duniya, idan baka sani ba tambayi Bafulatani. Duk dai hakan na faruwa ne saboda gubar nan ta Cyanide. Saboda haka, muna kira ga masu cin kwaki da su rinka jika shi da ruwan zafi, ko a yi teba a ci shi. Sannan a kiyayi cin danyen rogo dan kare kai daga mutuwa ko afkuwar cuta. Allah kyauta.

 

Namijin Goro Da Amfaninsa

Namijin goro da a Turance ake kira da ‘Garcinia Kola’ an fi samunsa a kasashen Afirka wadanda suka dauki dimbin shekaru suna amfani da shi a matsayin wani nau’i na magani a al’adun ‘yan Afirka.

Namijin goro na dauke da sinadiran ‘Dimeric Flabonoid’ wanda bincika ya tabbatar da yana magungunna da dama.

Ana noman namijin gori a kasar Nijeriya da Kongo da Gana da Senegal da Benin da sauransu.

Su kuma likitoci a nan Afirka, sun yi imani da cewa namijin goro na da sinadiran yakar wasu kwayoyin cuta na bakteriya da ma wadansu na birus,

Namijin goro na maganin kusan dukkanin cutukkan sanyi na kirji, kama daga yawan tari ko atishewa da cutukkan makogwaro da toshewar hanci da ciwon kai na gefe daya da cutukkan bututun iska.

Namijin goro na bada kariya ga garkuwar jiki a kan haka ne ya sa masu ilmin hada magani ke amfani da garinsa wajen hada magungunnan yaki da cutar tsida.

Yana saurin narkar da abinci don haka idan ka ji cikin ka ya kabe sai ka tauna namijin goro.

Yana da matukar amfani ga maza ma’aurata, don yana gyara takobin mai gida idan ya ballashe, musamman idan an hada shi da garin itaciyar jingsin da za ka yi wanda a cikin kwana ukku za ka ji yanda zakarinka zai rinka jan ka.

ga mata kuma akwai wani sirri a tare da namijin goro, a kan tarfa tiraren Musk Aisha aoriginal cikin garin sai a gauraya da lalle a daura, yana janyo sha’awar namiji zuwa ga matarsa. Kuma zai kara maki ni’ima ta musamman. Sai dai fa yana da matsala don yana hana bacci. Yana sa yawan jima’i. Yana kuma haifar da ramewa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: