Connect with us

Uncategorized

Girke girke: Yadda Ake Miyar Ridi

Published

on

Abubuwan Hadawa

 1. Ridi
 2. Kifi/nama
 3. Tattasai
 4. Albasa
 5. Attarugu
 6. Tumatur
 7. Spices

Yadda ake hadawa

Da farko ki wanke ridinki wadatacce ki shanya ya bushe, sai ki raba biyu, ki nika rabi, ki soya rabi. Ki soya shi har sai ya fara kamshi, sai ki sauke kar yayi baki.

Sai ki kawo kayan miyarki markadaddu wadatattu ki sa naman ragonki da gyararren kifinki busasshe ki soyasu tareda kayan miyarki, kada su soyu sosai.

Sai ki tsaida ruwa ki rufe. Idan ya tafasa ya yi kauri sosai sai ki kawo nikakken ridinki ki zuba kisa maggi da curry da gishiri da sauran spices sai ki rufe ki basu kamar minti goma.

Sannan sai ki kawo yankakken ugu leaf, kananan yanka, da yan kakkiyar albasa sai ki zuba, ki kawo ridinki soyayye wanda baki nikaba ki zuba ki jujjuya sai ki rufe, bayan minti biyar sai ki sauke.

Za a iya cinta da abinci kamar haka:

 1. Tuwon shinkafa
 2. Sakwara
 3. Sinasir
 4. Funkasau

A ci dadi lafiya.

Yadda Ake Dambun Nama

Abubuwan hadawa

 1. Nama/kaza
 2. Tarugu
 3. Albasa
 4. Tafarnuwa
 5. Seasoning
 6. Maggi
 7. Man gyada

Yadda ake hadawa

 1. Farko za ki wanke nama ko kaza ki zuba cikin tukunya ki zuba albasa da tarugu da tafarnuwa.
 2. Ki dora a wuta, ki barshi ya yi ta dahuwa kaman awa 4/5 yana dahuwa.
 3. Idan kin sauke, sai ki raba shi da kashi da kitsensa ko fata duka ki cire ki mayar da tsokar ki sa muciya ki tuke shi ki sa seasoning da spices.
 4. Sai ki zuba man gyada har ya rufe naman ki soya. Ba za ki daga ba ki na yi kina juya shi har ya yi.
 5. Sai a kwashe a saka a cikin abun tata a matse man. A tabbar ba sauran mai sai a zuba cikin siebe ko colander. A ci lafiya.

Yadda Ake Tsiren Kaza

A fannin girken girkenmu na Leadership Ayau, yau za mu koyi yadda ake tsiren naman kaza.

Abubuwan hadawa

 1. Tsokar kaza danye
 2. Yajin borkono
 3. Kayan kamshi
 4. Maggi chicken
 5. Albasa
 6. Tumatur
 7. Karas
 8. BBK machine
 9. Skewers

Yadda ake hadawa

Ki dauki yajin barkono ki ki sa a turmi ki kawo kayan kamshi da maggi iya dandanon da zai miki, ki sa ki kawo daddawa kadan ki sa gishiri kadan, ki sa ki daka ya daku sosai, sai ki ajiye a gefe.

Dauko tsokar kazar ki ki gyara ki yanka su sannan ki fadada yankan (yankan kamar yanda ake yanka na masu tsire) ajiye a gefe.

Sannan ki kara dauko kwano daban ki sa tsokar kazan ki sa ki kawo yajin ki barbada a kai, dauko albasa ki sa ki kara maggi iya dandanon da zai miki, sai ki juya komai ya hade da juna sai ki rufe ki sa a fridge nadan wani lokaci, ko ki bar shi ya kwana a ciki idan da dare ki ka hada shi.

Sai ki dauko hadin kazan ki sannnan ki kawo tsinken tsire ki dauko ki na sokawa a jikin tsinken ki na ajiyewa a gefe, ki kunna BBK machine na ki, idan ya yi zafi ki kawo hadin namanki, ki jera a kai kidan bar shi na dan wani lokaci sai ki juya. Haka za ki yi ta yi har sai ya gasu ki na iya yaryada man gyada da maggi mai ruwa idan ki na cikin gasawa, dan ya kara dandano.

Daga karshe, da zarar kinga ya gasu, sai ki sauke sannan ki yanka tumatur, albasa da karas a kai.

Karin bayani

Idan ki na so gashin naman ki ya dan yi yaji za ki iya idan ya yi rabin gasuwa sai ki sauke ki zuba yajin barkono ki a faranti, ki sake bade naman da shi, sai ki sake mayarwa akai ki karasa gasawa. A ci dadi lafiya.

Mai karatu wannan shine yadda ake tsiren naman kasa.

Yadda ake miyar ridi

Abubuwan Hadawa

 1. Ridi
 2. Kifi/nama
 3. Tattasai
 4. Albasa
 5. Attarugu
 6. Tumatur
 7. Spices

Yadda ake hadawa

Da farko ki wanke ridinki wadatacce ki shanya ya bushe, sai ki raba biyu, ki nika rabi, ki soya rabi. Ki soya shi har sai ya fara kamshi, sai ki sauke kar yayi baki.

Sai ki kawo kayan miyarki markadaddu wadatattu ki sa naman ragonki da gyararren kifinki busasshe ki soyasu tareda kayan miyarki, kada su soyu sosai.

Sai ki tsaida ruwa ki rufe. Idan ya tafasa ya yi kauri sosai sai ki kawo nikakken ridinki ki zuba kisa maggi da curry da gishiri da sauran spices sai ki rufe ki basu kamar minti goma.

Sannan sai ki kawo yankakken ugu leaf, kananan yanka, da yan kakkiyar albasa sai ki zuba, ki kawo ridinki soyayye wanda baki nikaba ki zuba ki jujjuya sai ki rufe, bayan minti biyar sai ki sauke.

Za a iya cinta da abinci kamar haka:

 1. Tuwon shinkafa
 2. Sakwara
 3. Sinasir
 4. Funkasau

A ci dadi lafiya.

Yadda Ake Dambun Nama

Abubuwan hadawa

 1. Nama/kaza
 2. Tarugu
 3. Albasa
 4. Tafarnuwa
 5. Seasoning
 6. Maggi
 7. Man gyada

Yadda ake hadawa

 1. Farko za ki wanke nama ko kaza ki zuba cikin tukunya ki zuba albasa da tarugu da tafarnuwa.
 2. Ki dora a wuta, ki barshi ya yi ta dahuwa kaman awa 4/5 yana dahuwa.
 3. Idan kin sauke, sai ki raba shi da kashi da kitsensa ko fata duka ki cire ki mayar da tsokar ki sa muciya ki tuke shi ki sa seasoning da spices.
 4. Sai ki zuba man gyada har ya rufe naman ki soya. Ba za ki daga ba ki na yi kina juya shi har ya yi.
 5. Sai a kwashe a saka a cikin abun tata a matse man. A tabbar ba sauran mai sai a zuba cikin siebe ko colander. A ci lafiya.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: