Connect with us

LABARAI

Gwarzon Dan Siyasa Shi Ne Mai Cika Alkawari Da Rike Amana ­—Buhari

Published

on

A jiya Juma’a ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘Yan majalisar jihar Katsina da su kasance sun tabbata a kan hanyar gaskiya da rike amanar al’ummar da suka zabe su, zuwa wannan matsayi da suke kai na majalisa.

Jawabin wanda mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya yi, ya bayyana hakan ne a Abuja, wanda  kuma ya ce, shugaban kasar ya fadi hakan ne lokacin da shugabannin majalisar dokokin jihar  ta Katsina karkashin jagorancin shugaban majalisar, Tasiu Maigari, suka kai ziyarar gaisuwar salla ga Shugaban kasar a garin Daura ta jihar Katsina jiya Juma’a.

Kamar yadda shugaba ya ce. Babban dalilin tsayawa takara har a zabi mutum shi ne, domin ya yi wa al’umma hidima. Saboda haka, dole ne gwarzon dan siyasa ya kasance mai cika alkawari da rike amanar jama’ar da suka zabe shi. “Kasancewarka wanda al’umma suka zaba dole ka zama mai gaskiya, ka zama mai adalci a kowane lokaci. Shugabanci a gida ko na al’umma a matakai daban-daban nauyi ne da aka dorawa mutum wanda ya zama wajibi ya yi kokarin sauke wannan nauyin ta hanyar tabbatar da adalci a tsakanin mutanensa’’ in ji shi.

A karshe, Shugaban kasar ya bukaci ‘yan majalisar su zama masu hangen nesa tare da yin aiki tukuru domin sauke nauyin da aka dora musu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: