Connect with us

KIWON LAFIYA

Hanyoyi  Biyar Na Yadda Kwakwa Ke Amfani A Jikin Dan’Adam

Published

on

Kwakwa dai kamar yadda aka sani wata diyar itace ce mai matukar amfani ga rayuwar bil’adama, kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka bayyana. Kwakwa na daya daga cikin ‘ya’yan itace mai matukar amfani, saboda da irin sinadarin da Allah Ubangiji ya zuba cikin ta.

Kwakwa na dauke da ruwa cikin ta kana har ila yau ana bare jikin kwakwa sannan a ci. Kwakwa ya rabu kashi biyu, akwai kwakwar manja kana akwai kwakwa wace bata dauke da manja. Dukkanin nau’oin kwakwa dai na dauke da sinadarai da suke da matukar amfani ga rayuwar bil’adama kamar yadda masana suka bayyana.

 

Wasu daga cikin alfanun kwakwa ga rayuwar bil’adama sun hada da:

  1. An bayyana kwakwa da yana kara lafiyar garkuwar jikin bil’adama, kasancewa yana na dauke da sinadaran antibiral, antibacterial, antifungal da kuma antiparasite.
  2. Har ila yau masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana kwakwa da cewa yana kara lafiya da walwallan jiki ga bil’adama.
  3. Kwakwa na dauke da sinadaran bitamins wadanda ke taimaka wa sassan jikin bil’adama dake narkar da abinci ba tare da gajiyawa ba.
  4. Har ila yau masana sun bayyana kwakwa da yana matukar taimakawa masu dauke da cutar suga (diabetes), kana yana samar da kariya ga wadanda basa dauke da cutar.
  5. Saboda sinadarin “insulin” dake cikin kwakwa, masana sun bayyana kwakwa da yana rage barazanar kamuwa ko radadin cutar kansa (cancer) a jikin bil’adama.

Wadannan sune kadan daga cikin amfanin da kwakwa ke yi wa mutane.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: