Connect with us

ADABI

IIiya Dan Mai Karfi (6): Na Muhammadu Ingawa

Published

on

Ci gaba daga makon jiya

 

ILIYA YA SAKE SHIGA DUNIYA

Mutanen da ke wurin suka ce wa mai giyar nan, idan ba ka ba shi ba, zai mutu, ka ga ka jawo wata rigima ke nan,: Aka debo giya aka sa wa Iliya a baki, nan da nan ya farfado. Aka karo masa mai yawa ya sha ya koshi, har ya bugu.  Shi ke nan sai ya shiga kantin giya ya yi kwanciyarsa, ya yi ta sharar barci. Da dare ya yi kwarai masu kantin suka ta da shi, ya ki tashi, sai suka rufe kantin da shi ciki.  Tun da asuba Iliya ya tashi, ya sa kafa ya buge kyauren kantin. A cikin kantin akwai wadansu gangunan giya manya-manya, wadanda komai karfin kato ba zai iya daga ganga guda ba, balle ya yi tafiya da ita. Iliya ya kwashi guda uku, ya makale ko wace daya a hammata, ya rika tura daya da kafarsa, yana tafe yana cewa, Duk wanda ke so ya sha giya ya zo nan, har wanda ba ya sha ma in yana so ya zo.

Daga can masu giya suka ji, suka biyo shi, suka yi, suka yi, su kwace gangunan giyarsu, abu ya faskara.

Sai suka tafi suka kai kara wurin Alkali. Alkali ya aika aka rarraso Iliya. Da jin labarin, sai Waldima ya tsargu, ya tabbata ba mai iya yin haka sai Iliya. Don haka da zuwansa sai ya ce, Haba Iliya, da ma ka komo cikin kamarka ta sosai. Sai Iliya ya bushe da dariya, ya komo kamar yadda kowa ya san shi. Ya biya masu giya kudinsu, ya ba su sauran giyar. Da dare ya yi, bayan an gama hira, duk fadawa sun watse, sai Waldima kadai da Iliya, Waldima ya ce masa, Ina so ka taimake mu, ka kubutar da mu daga sharrin wani rikakken dan hari, maridi, wanda ake kira Falalu. Ko’ina ya ratsa cikin kasar nan sai ya rika kwace, yana raba mutane da dukiyarsu, ya kuma ba su kashi. Ya dame mu kwarai, ba mu kuwa da wani wanda zai iya tararsa, sai kai kadai. Iliya ya yi murmushi, ya gyara zama, ya murza gashin baki, ya san ranarsa ta zo, ya ce wa Sarki, Allah ya ba ka nasara, an gama. Allah dai ya ba mu sa’a. Ina so daga cikin jarumanka, da kake takama da su ka zabo mini shida mu tafi tare. Amma mutanen nan guda shida ba don komai Iliya yake bukatarsu ba, sai don ya jarraba jaruntakarsu. Waldima ya umarci jarumai shida su shirya su bi Iliya. Da lokacin ya yi, jaruman nan suka shirya, Iliya na gaba suna biye da shi, suka nufi hanyaar da Falalu ke wucewa.

 

ILIYA YA HADU DA FALALU

Can wajen asuba, sai suka ji motsin Falalu tafe, yana keta itatuwa kamar toron giwa. Yana tafe yana shakar iska abinsa, don ya san ba mai iya tarensa da fada. Ya zo ya wuce ta kusa da inda su Iliya suke boye, bai gan su ba.

Sai Iliya ya ce da jaruman nan, Wa zai iya binsa ya ga inda ya nufa? In kuma ya ga da dama, ya tone shi da fada?

Duka sai suka yi shiru, aka rasa wanda zai ce zai bi shi. Sai wannan ya dubi wannan, wancan ya dubi wancan. Iliya ya dubi babbansu ya ce ya tafi. Jarumin nan bai yi gardama ba, ya tashi ya kara jan majayin dokinsa, ya hau, ya bi sawun Falalu. Amma duk zuciyarsa tana dar-dar, yana tafe yana kulle-ullen yadda zai yi, a zuci. Ya dai tabbata idan suka yi ido da ido da Falalu, shi ba zai kwana ba. Ya yi ta tafiya har ya fara hangen Falalu.

Can sai ya hangi Falalu ya tsaya ya dubi kansa ya dubi kayan fadansa, ya dubi dokinsa, ya yi dariya, ya zaburi dokinsa kadan, ya yi tabi, ya jefa mashinsa sama, ya bi ya café, yana kirari yana cewa, Yau ko da Iliya ta hada mu ma kara! Yau ina zan gamu da Iliya!

Sa’ad da jarumin nan ya ji Falau ya ambaci Iliya sai ya tuna shi ma jarumi ne,nan

da nan zuciyarsa ta motsa. Daga can nesa, ya ce, Falalu! Kayarka ta sha karya, maza bisa kanka. Idan ka sake kuka yi arba da Iliya, sai dai wani ba kai ba!

Falalu fa ya juyo a fusace ya ga mai magana. Ya yi, wata irin kururuwa mai ban firgici, kamar aradu ta fadi.

Sai hayaki ya rika fita daga bakinsa, har da wata irin walkiya kamar hadari ya taso. Akwai wata korama kusa da shi, nan da nan sai ruwanta ya kada yana kumfa. Ya nufi jarumin nan a sukwane, shi kuma ya juya a guje ya koma wurin su Iliya. Saboda sauri har dokinsa ya yi sassarfa ya fadi.

Ya dai tashi da rawar jiki ya sake hawa ya ci gaba da sukuwa har ya kai wurin

Iliya, yana haki kamar ransa zai fita. Da ya farfade kadan, ya fada wa Iliya abin da ya faru.

Duk abin nan Iliya zaune ya ke. Ko da ya ji labarin kuwa sai ya yi murmushi, ya kara kishingida, ya rika wasa da kafarsa. Ya dubi jaruman nan ya ga duk sun rude

kowa ido ya fito. Ya ce, Allah Sarki, tsufa ya zo mana ga shi kuwa ba mu da magada. Sai ya yi wuf ya tashi ya tafi wurin Kwalele, ya shafe shi ya yi masa kirari, Kwalele dokin Iliya, Kwalele dokin yaki. Ba ni saishe ka, ba ni kuwa ba

da aronka! Kwalele ya yi haniniya kamar ya san abin da Iliya ke fada.

Daga nan Iliya ya dauko sirdi ya aza ya daura tamau. Ya sabi kulki ya rataya takobin Wargaji, ya dau mashi da kwari da baka, ya zabura ya nufi Falalu. Da suka kusa haduwa shi Iliya ya fara hargowa, yana cewa, Kai lalataccen maridi, barawo. Don me ka shigo kasarmu ba da izimmu ba! Falalu ya kara harzuka, ya cika

da haushi. Za mu ci gaba mako mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!