Connect with us

LABARAI

Lawan Ga Buhari: Zamu Tabbatar Da Nasarar Gwamnatinka

Published

on

A jiya ne, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya jagoranci tawagar shugabannin majalisar Dattawa wajen wani taro na musamman da Shugaban kasa Buhari, a Daura, ta Jihar Katsina.

Shugaban da ‘yan majalisar sun shiga wani taron sirri wanda ya dauke su kimanin awa guda.

Da yake Magana da manema labarai, shugaban majalisar Dattawan cewa ya yi. tabbas za su dage ne a kan aikin na su domin tabbatar da duk wasu tsare-tsaren gwamnati.

“Za mu zage damtse ne a kan aikin namu, muna son kowa ya yi damarar yin aiki. Shugaban kasa zai kare aikinsa ne a shekarar 2023, a inda muke fatan kamar yanda yake fatan barin wasu ingantattun tsare-tsare a karshen mulkin na shi, muna fatan mu shiga cikin tarihin samun nasarar aiwatar da dukkanin tsare-tsaren na shi.

“Hanya daya da za mu tabbatar da wadannan tsare-tsaren ita ce dagewa a kan ganin duk wanda aka ba shi alhakin gudanar da wani aiki ya yi wannan aikin kamar yanda aka danka ma shi amanar shi, za mu yi aiki tare da Ministoci da shugabannin hukumomi domin tabbatar da dukkanin tsare-tsaren gwamnati suna tafiya yanda suka dace, mu kuma tabbatar da dukkanin dokokin da muka zartas anyi aiki da su sau da kafa,” in ji Lawan.

Ya kara da cewa; “Mun sake jaddada aniyarmu ga shugaban kasa, na cewa za mu yi da gaske a bisa kyakkyawar manufa a kan duk wani abin alherin da zai aiwatarwa ‘yan Nijeriya a wannan karon na mulkin na shi. Dangane kuma da Ministoci masu zuwa, Lawan ya ce, Wadannan Ministocin kwararru ne ainun, masu kishin kasa, da aniyar yin aiki. Kowannen su ya nuna aniyarsa ta yin aiki tukuru.

Shugabannin majalisar da suka gana da shugaban kasan sun hada da, Shugaban majalisar, da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi; Mataimakin shugaban masu rinjaye, Sanata Ajayi Borrofice; mataimakin masu tsawatarwa, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi; shugaban marasa rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe; mai tsawatarwa marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda da mataimakin mai tsawatarwa marasa rinjaye, Sanata Sahabi Alhaji Ya’u. da kuma wasu sanatoci guda biyu daga Jihar Katsina, Bello Mandiya da Ahmad Babba Kaita, duk suna cikin wadanda aka kai ziyarar da su. in ba a manta ba, mataimakin shugaban majalisar ta Dattawa, Odie Omo-Agege, ya je Daura din a ranar Talata.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: