Connect with us

WASANNI

Me Siasia Ya Yi FIFA Ta Dakatar Dashi Har Abada?

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da tsohon kociyan Najeriya Samson Siasia saboda ya amince ya sayar da wasa bayan da aka gudanar da wani bincike akan zargin da ake masa a kwanakin baya.

Siasia ya zamo kocin Najeriya daga shekarar 2010-2011 sannan kuma na wani dan lokaci a shekara ta 2016, sai dai babu tabbas a kan lokacin ya aikata wannan laifin kamar yadda rahoton Fifa ya tabbatar.

Ya kuma taba kasancewa kociyan tawagar kasar ta ‘yan kasa da shekara 20 da kuma 23 kuma ya kasance daya daga cikin masu koyarwar da sukayi bajinta wajen koyar da ‘yan wasan Najeriya a matakai daban-daban.

A wata sanarwa da ta fitar, Fifa ta ce an samu Siasia da laifin amincewa ya karbi na-goro domin sauya sakamakon wasanni kuma wannan mataki yana da alaka da bincike mai zurfi da Fifa ke yi kan halayyar Wilson Raj Perumal, wanda aka samu da laifin sayar da wasa a kasar Singapore.

Siasia ne dan Afirka na uku da Fifa ta dakatar dangane da batun na Perumal bayan da aka dakatar da tsohon jami’in kwallon Saliyo Abu Bakarr Kabba da na Botswana Mooketsi Kgotlele a watan Yuli, na tsawon shekara biyar da kuma har abada.

A lokacin da yake buga kwallo, Siasia ya lashe gasar Kofin Afirka a 1994 da Super Eagles ta Najeriya, inda ya buga wa kasar nan wasa sama da sau 50, sannan ya ci kwallaye 16 kamar yadda kididdiga ta nuna.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: