Connect with us

LABARAI

NAHCON Ta Taya Saudiyya Murnar Samun Nasarar Aikin Hajjin Bana

Published

on

Shugaban Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON), Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad, ya taya kasar Saudiyya murnar kammala aikin Hajjin bana cikin nasara, duk da dimbin al’ummar da suka halarci kasar daga sassan duniya domin yin wannan ibada ta Hajji.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, a wata takarda da jami’ar hulda da jama’ ta Hukumar Fatima Sanda Usara, da rabawa manema labarai.

Haka kuma Barista Muhammad ya jinjinawa ma’aikatar kula da Umara bisa kwarewar da suka nuna, wanda masu gudanar da ibada suka yi cikin kwanciyar hankali.

Ya yi wannan bayanin ne a Mina ganin yadda aka gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali, sannan kuma Alhazai suka dawo Makka cikin nutsuwa.

Sannan ya nuna gamsuwarsa game da yadda aka samar da masaukai ga bakin da suka shiga kasar ta saudiyya domin yin aikin Hajjin na bana.

An samawa Alhazan Nijeriya kyakkywan masauki, wanda haka ya sa suka samu walwal a dukkan tsawon zaman da suka yi.

Har ila yau, Muhammad ya yaba da kokarin da sashin sufuri ya yi na tafiyar na zirga-zirga ba tare da wata matsala ba.

A karshe ya yi fatan cewa, Kamfanonin jiragen saman da ke da alhakin komawa da Alhazai za su koma da su ba tare da bata lokaci ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: