Connect with us

DAGA TEBURIN EDITA

Sakon Fatan An Yi Sallah Lafiya Daga ‘Yan Kungiyar RAYAAS

Published

on

Barka Da Assalamu alaikum Edita Barka da aiki da fatan an yi Sallah lafiya, Allah ya maimaita mana amin. Bayan haka muna son a ba mu damar mika sakonnin gaishe-gaishenmu ga ‘yan uwa da abokan arziki da ke wannan kungiya tamu mai albarka wato RAYAAS, da fatan Allah ya kara maka basira amin.

 

Rayuwarmu A Yau Youth Awareness Association

Amadadin Shugaban kungiya na kasa, Babban  Secretary kungiya na kasa, Secretary Tsare tsare na Kasa. Da sauran daukacin Shuwagabannin wannan kungiyar mai albarka.

Muna amfani da wannan damar domin yiwa daukacin al’ummar Kasar nan Musamman Members na wannan kungiyar barka da sallah, tare da fatan Allah ya karbi ibadun da muka gabatar a ciki.

Haka kuma muna kara amfani da wannan dama, domin kira ga members na wannan kungiyar dasu dukufa wajen yi wa wannan kungiyar addu’o’in nasara da fatan alheri a bisa kudurorin ta na alheri. Ubangiji Allah ya karbi ibadunmu, ya kuma kara kawo muna zaman lafiya a jihohinmu da Kasarmu baki daya, a yi shagulgulan sallah lafiya.

Daga Kabiru Garba Gusau Sakatare Janar Na Kasa, amdadin Shugaban Kungiya na Kasa Shehu Na Amo Dange.

 

Rayuwar Mu A Yau Youth Awareness Association (RAYAAS) Sokoto Chapter.

Jajantawa Ga Dan Uwan Mu

Muna mika sakon jaje ga DSM na wannan gidan Malam Suleiman Ibrahim (J Na’inna), kan ibtila’in da ya same shi na faduwar katangar sa sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi a wani dare zuwa wayewar safiya. Muna rokon Allah da ya mayar masa da mafificin alkhairi, ya kuma kare afkuwar hakan a gaba. Domin yi masa jaje sai a kira shi da wannan lambar waya: 07037354311. Maiyaki Labaran Dange, PRO 1 amadadin Alhaji Sirajo Madawaki Sokoto, (Turakin RAYAAS) Shugaba na Jihar Sokoto.

 

Assalamu alaikum Edita

Amadadin Shugaban riko na kungiyar rayaas reshen Babban Birnin Tarayya Abuja Alhaji Nasiru Isa Garun Malam nake isar da sakon barka da Sallah ga daukacin ‘ya’yan wannan kungiya mai albarka na Kasa baki daya Allah ya maimaita mana amin. Kazalika muna mika sakon ta’aziyarmu ga dan uwa Shugaban Jihar Gombe Affan Ibrahim da ma dukkan mambobin kungiya baki daya Allah ya jikan musulmin da suka riga mu gidan gaskiya, mu kuma idan tamu ta zo ya yi mana kyakkyawar cikawa amin. Sanarwa daga Auwal Mu’azu PRO RAYAAS FCT Abuja.

 

RAYAAS Media Commitee

Ina yi wa daukacin mambobi da Shugabannin wannan kungiya mai albarka Albishir da cewa, In Sha Allahu za mu kafa: RAYAAS MEDIA COMMITEE, inda za mu zabo zakakuran mambobi jajirtattu daga kowace jiha, domin su taimaka mana wajen kara yada manufofi da kuma ayyukan kungiyar RAYAAS a kasa baki daya, musamman ta kafafen sada zumunta na zamani.

Yanzu haka muna ci gaba da tantance mutanen da ya kamata mu dorawa wannan gagarumin aiki, da zaran mun kammala zamu bayyana muku sunayensu.

A karshe muna kara godiya zuwa ka daukacin mambobi da Shugabannin wannan kungiya ta Kasa baki dayanku bisa gudummuwa da goyon baya da kuke ba mu, Allah ya kara dankon zumunci. Auwali Adamu Differences, Sakataren Tsare-Tsare Na Kasa baki daya.

 

Rayuwarmu A Yau Youth Awareness Association

Sakon Barka Da Sallah Tare Da Tunatar Da Junanmu

Kamar yadda kuka sani wannan kungiyar mun nemi taimakon ko wane mamba musamman wadanda suka yi layya cewa, muna bukatar sadakar fata domin ci gaba da aikin alherin da muka sa a gaba, kan haka muke  kara tunatar da kowa cewa game da kudaden fatar, *kowane member ko masu rike da mokamai na Kasa ko na Jiha ya damka wa Shugabansa na Jiha, ko fatar ko abui da Allah ya hore masa  duk Shugaban da ya kammala karbar fatun layya ko kudin fatar  zai iya saida fatar  sannan sai ya tura kudin ta wannan asusun na kungiya kamar haka: Acc No-5960318018 Acc: Name Rayuwarmu A Yau Youth Awareness Association

Bank FCMB. Allah yayi muna jagora da taimako amin. Sanarwa Kabiru Garba Gusau

Sakatare Janar RAYAAS, a madadin Shugaban kungiya na Kasa Shehu Na Amo.

 

Jinjina Ga LEADERSHIP A Yau Lahadi

Assalamu alaikum Edita

Bayan gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga ma’aikatan gidan wannan jarida mai albarka wato LEAFERSHIP A Yau Lahadi, sabo da irin gagarumar gudummawar da suke bayarwa domin ci gaban wannan kungiya tamu mai albarka Allah ya saka musu da alkairi amin, Allah ya kara daukaka gidan wannan jarida tare da ma’aikatanta amin. Sannan kuma ina yi wa duk kannin shuwagabannin wannan kungiya ta mu ta RAYAAS  da duk kuma duk kannin mambobin ta na kasa baki daya barka da Sallah hade da duk musulmin duniya barka Allah ya karbi dakkannin ibadun mu amin.

San nan kuma ina mika sakon ta’aziyata izuwa ga Shugaban kungiyar rayuwarmu a yau naka Alhj. Shehu na Amo dange uban dawakin dange, Sarkin Bauran Dange da shugaban Jihar sokoto hade da mambobin wannan kugiya ta rayaas na sokoto bisa rasuwar baban mu wato Alhaji Mode sarkin fawan dange muna yi masa adu’a Allah ya jikan sa ya yi masa rahama amin, Allah ya ba wa iyalansa hakurin rashinsa, Allah ya albarkaci abin da yabari amin.

Akarshe ina mika sakon ta’aziya ta zuwa ga Shuganan Kungiyar RAYAAS reshen Jihar Gombe Malam Affan Ibrahim a bisa raswar kaninsa, Allah jikansa Allah ya gafarta masa dukkannin zunubansa Allah ya ba wa iyalansa da ‘yan uwansa hakurin rashinsa amin, sako daga Shugaban kungiyar RAYAAS na Arewa ta Tsakiya Nasiru isa Garun Malam daga Babban Birnin Tarayya Abuja. Allah yayi muna jagora da taimako amin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: