Connect with us

WASANNI

Salah Zai Sake Sabon Kwantiragi A Liverpool

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tana kokarin karawa dan wasa Muhammad Salah sabon kwantiragi wanda zai zaunar dashi a kungiyar na da shekaru da dama kuma zai kasance dan wasan da zaifi kowanne dan wasa daukar albashi a gasar firimiyar Ingila.

Salah dai ya kasance daya daga cikin dan wasan da yafi kowanne dan wasa hazaka a gasar firimiya tun bayan komawarsa kungiyar daga Roma a shekara ta 2017 inda ya zura kwallaye 72 cikin wasanni 107 daya bugawa Liverpool.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce take zawarcin dan wasan dan asalin kasar Masar sai dai kokarin da Liverpool takeyi na kara masa sabon kwantiragi zaisa Madrid din su hakura da nemansa.

A shekara ta 2018 dai Liverpool ta karawa dan wasan sabon kwantiragi sai dai sakamakon neman da wasu daga cikin manyan kungiyoyi suke yiwa dan wasan zaisa Liverpool din ta kara masa sabon kwantiragi wanda zaisa yayi tsadar da kungiyoyi zasu hakura da zawarcinsa.

A kakar wasansa ta farko ya zura kwallaye 44 sannan a kakar wasa ta biyu kuma ya zura kwallaye 27 wanda hakan yake nufin yana yawan zura kwallaye a raga sannan kuma akwai kungiyoyin da suke bukatar dan wasa irinsa.

A jiya ne dai tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Garry Nebille, ya bayyana cewa dan wasan zai iya barin Liverpool a kakar wasa mai zuwa saboda akwai kungiyoyin da zasu nemi dan wasan kuma zai bukaci tafiya saboda yayi abinda yakamata a Liverpool
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: