Connect with us

WASANNI

Sanches Yana Son Barin Manchester United Kafin A Rufe Kasuwar ‘Yan Wasa

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Aledis Sanches, ya bayyana cewa yana fatan ganin ya rabu da kungiyar kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta wannan kakar wadda za’a rufe ranar 31 ga wannan watan na Agusta.

Sanches dai yana shan wahalar buga wasa a Manchester United tun bayan komawarsa kungiyar daga Arsenal a watan Janairun shekara ta 2018 inda ya zura kwallaye uku cikin wasanni 32 daya buga a gasar firimiyar ingila.

Manchester United dai ta shirya rabuwa da dan wasan sai dai har yanzu bata samu kungiyar da zata iya biyan kudin dan wasan ba wanda hakan yasa har yanzu yake zaune a kungiyar sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa ya fara Magana da wasu kungiyoyin a kasar Italiya.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa Sanches yanason komawa kasar Italiya da buga wasa inda yafara Magana da kungiyar kwallon kafa ta Roma domin ganin sun daidaita duk da cewa a baya ya bugawa kungiyar Udinese wasa.

Saura shakara uku da rabi kwantiragin dan wasan ya kare da Manchester United sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa United din ta shirya biyan wani bangare daga albashinsa domin dai gani yabar kungiyar.

Kociyan Manchester United, Ole Gunner Solkjaer dai ya bayyana cewa yana fatan dan wasan zai zauna domin taimakawa kungiyar kuma ya dawo da kokarinsa sai dai abune mai wahala shugabannin kungiyar su amince ya cigaba da zama saboda yawan albashin da yake dauka.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: