Connect with us

ADABI

Sharhi Da Fashin Baki Akan Wakokin Shata Na Sarkin Bai Na Katsina Alhaji San Stores

Published

on

Bismillahirrahmanir rahim,

An yi wasu lokuta da Dokta Mamman Shata Katsina kan tafi Katsina a tsakanin 1946 da 1947 ya tare, sai ya yi kamar wata guda a cikin garin. A wannan ‘kwamba’ sai kullum da dare ‘yan birni da suka isa su gayyace shi wasa a unguwar Sararin Kuka, a taru a gindin wata itaciyar cediya. Nan yake yin wasan dare, tun daga farkon dare har sai gari ya waye. Nan ne wurin da ‘yan birni ke taruwa hira, ana kallon wasannin makada. A daidai wannan wakati sun fara sabawa da Alhaji Sani Stores sama-sama, amma kuma ba shi ne sababun zuwan sa birnin ba.

Don haka dangantakar Shata da marigayi Alhaji Sani Stores ta samo asali ne tun daga 1947 lokacin da makadin ya zo Katsina bukin auren fari na Kabiru Usman Wakilin Doka (wanda ya zama Sarkin Kachina daga bisani), da kuma 1951 lokacin da Shatan kan je Katsinar wasan sallah. Duk a cikin ‘ya’yan Sarki da wadanda suka shafi sarauta ba wanda hankalin Shatan ya kwanta da shi kamar Sani Stores. To wannan amana da mu’amulla ta sanya Haji Sani Stores ya zame shi ne ma ubangidan sa na farko a Katsina. Kafin zamanin Sani Stores, Shata ba shi da ubangida a Katsina. Duk sallah, Shata za ya tafi gidan Alhaji Sani Stores ya yi wasa, kuma da rana, bisa ga umurni da amincewar shi Alhaji Sani Stores. Wannan ya nuna Shata bai fara sani ko tunanin gidan wa za ya je ya yi was aba sai gidan Store Sani.

Kafin wannan lokacin, Shata bai taba yin wasa a gidan wani mutum ba kuma da rana, saidai a otel da kuma dandali (watau a unguwar Sararin Kuka)  Dalili ? Saboda a daidai wannan lokacin, masu rie da sarautu, galiban ba su da karfin dauko makadin zuwa gidajen su in ba Sani Stores ba. Idan ya zo ya yi masa da rana, za ya samu kyautar riguna da kudi da suka kai darajar fam biyar a matsayin sallama daga Alhaji Sani Stores. A lokacin duk fadin Katsina ba mai fam daya ma da za ya iya ba makadin, don lokacin ba kudi, domin wuya suke yi, kuma ba mota.

Wannan damar ce ta sanya daga baya bayan jama’a sun fara yi masa yawa a birni sai dole Sani Store ke nuna masa mutanen arziki. Ya ce masa : ‘je ka gidan wane ka yi wasa’, ko kuma ‘kada ka je gidan wane wasa saboda dalili kaza da kaza’. Ma’ana, sai da izinin Store Sani Shata kan tafi gidajen wasu masu hali ya yi wasa, kamar gidan su Abu Darma, gidan su Abu Duwan, gidan su Na Daunaka mai aljana, gidan Turaki Dan uwan Damale, gidan Bature jikan Dada, gidan Bature Dan Yamai, da sauran su.

Marigayi Alhaji Halilu Sararin Kuka (yaron Shata) da Sa’in Katsina Amadu Na-Funtuwa da mahaifiyar Abba Na-Titi da marigayi Bature Sarkin makadan Bakori da wata tsohuwa matar marigayi Ibrahim Ladan Fari, da kuma wata tsohuwa ‘yar uwar Abu Darma direba sun yi mani karin haske akan karakainar sa a Katsina a lokacin.

Don haka, a wannan tsakani, kafin idanun makadin su bude a kwaryar Katsina Haji Sani Stores ke daukar dawainiyar cin sa da shan sa da suturar sa, gami da hidimar yaran sa. Stores ya zama kamar shi ne retailership  na makadin da rundunar sa.

Shata kan tafi Central Office watau Ofishin N.A. ko (Natibe Authority) wurin su Alhaji Sani Stores ya zauna a yi hira da shi, a lokacin Stores yana aikin akawu a Store na N.A.  To ka san makadin yana da wata irin kwakwalwa ta nazarin mutum. Duk lokacin da ya zauna tare da mutum ba ya yin komi sai karantar halayen sa da kuma mu’amullar sa da mutane. Ta nan ya gane yanda Alhaji Sani Stores ke hulda da sauran ma’aikatan N. A.

Cikin 1966 sai aka nada Haji Sani Stores Sarkin Bai na Katsina. Wannan ta sanya dole Shata ya zo. Ya yi masa waka har kala biyu. Wakar farko da ya yi masa mai taken Bakandamiya ko Alo alo, ya nuna wadancan halaye da yake gani daga wajen sa lokacin da yake zuwa Central Office yawo wajen sa. Bakandamiya dai ita ya fara yi masa. Ko da ya ke wadda ya fara yi masa ta farko tana da tsawo kuma an dauke ta amma yanzu babu ita, wannan da ake ji wadda ta yawaita a hannun mutane ‘yar gajera ce ko gutsurarra wadda ya yi masa daga baya, don Shatan na ganin cewa waccan ta farkon tana neman bacewa. Wanda ya dauki faifan waccan Bakandamiya ta farko shi ne Alhaji Iro Gawo,  tsohon jami’in ma’aiikatar watsa labaru na rusashshiyar Jihar Arewa ta Tsakiya.

Ita ko Bakandamiya sunan ta ‘uwar wakoki’ kuma ba kowa ake yi ma ita ba. Shata da kan sa (1971) ya ce wakar ‘mazan jiya’ ce. A wurin makadin, ba ka zama ‘mazan jiya’ ko k cancanci a yi maka wakar Bakandamiya sai idan ka kasance kana da abubuwa guda biyu: ka dade kana mu’amulla da mutane, tare da kauda fuska akan wata cutarwa da suke yi maka, ko da kuwa suna cutar da kai din, sai kuma yawan alheri, matukar Allah Ya yi maka arziki ko Ya ba ka abin yin alherin. Duk wanda aka yi ma wakar Alo alo…’, to tabbas yana da wadannan halayen. Sani Stores ya same su. Ya kan ce; Mai daraja na Korau Store Sani, watau, duk wanda jibanci sarautar Katsina, dole ake jingina shi da sunan Korau, saboda Sarkin Katsina Muhammadu Korau (1427-1487) shi ya fara musuluntar da mutanen Katsina, tare da taimakon wasu waliyyai, irin su Sheikh Abdul Maghil. Sannan ya ce:  Mai daraja, a gaishe ku ‘yan Birni…’/ Cewa mutanen birnin Katsina sun yi dace da har suka samu mutane irin su Sani Stores. Don ya ce ‘a gaishe ku’, ba wai yana nufin gaisuwa ga ‘yan birni ba, yana nufin arzikin birni ya kai tunda ga irin su Sani Stores a cikin Katsina. Itama kuwa kamar ‘daraja’ ga Shata tana nufin mutum dottijo wanda ya rike amanar baitulmali bai dauki kudin jama’a ba. Sannan sai ya ce: Nai maka gargadi Haji Store Sani…’/, ma’ana yana bas hi shawara irin yanda mahaifin sa ya yi zama da su Sarki Usman Nagogo cikin amana ba wanda ya saba ma wani, to shima ya gaji mahaifin sa, cewa kada kwadayi ko zari ta sa ya yi wani ko wata almundahana da za ta sanya Sarkin Birni ya tsane shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!