Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Bala Da Babiya’

Published

on

Suna: Bala Da Babiya.

Tsara labari: Nasir S. Gwangwazo.

Kamfani: G-Top Multimedia.

Daukar Nauyi: UK Entertainment.

Shiryawa: Sani Mai Iyali.

Bada Umarni: Ibrahim Bala.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Sadik Sani Sadik, Fatima Abdurrahaman, Ibrahim Bala, Hauwa M. Auwal, Nabila Muhammad, Dauda Adakawa, Baba Labaran da sauransu.

Fim din Bala da Babiya, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wasu masoya masu tsananin kaunar junansu wato Bala (Ibrahim Bala) da kuma Babiya (Fatima Abdurrahaman). Su dai Bala da Babiya sun dade suna kaunar juna tun lokacin da ita Babiya ta ke karamar yarinya, kowa ya san su tare kuma ya san da soyayyarsu. A kodayaushe burinsu shi ne ganin sun mallaki junansu a matsayin miji da mata.

Burin Bala na mallakar Babiya ya fara samun tarnaki tun daga lokacin da Alhaji Auwalu( Sadik Sani Sadik) ya fara bibiyar soyayyar Babiya. Alhaji Auwalu mai kudi sosai sai dai ya kasa samun cikakkiyar soyayyar Babiya, sakamakon soyayyar gaskiyar da ta ke yi wa Bala. Duk da cewa ba ta kaunar Alhaji Auwalu, amma ta na karbar abu idan ya bata kuma tana iya tambayar sa wani abu idan ta na da bukata. Sai dai shi a nashi bangaren, Bala ba ya jin dadin yadda Babiya ta ke tsayawa ta na sauraren Alhaji Auwalu.

Tsananin kishin da Bala ya ke yi a kan Babiya ya sa ya fara shiga halin kokonto domin kuwa shi ba shi da kudi, kuma ga mai kudi ya tunkaro soyayyarsa gadan-gadan. Amma ita Babiya ma hasali ta na sauraren Alhaji ne domin ta samu ta samu kudade a jikin shi, wanda za ta bawa Bala domin ya je ya nemi aurenta a wajen kawaunta. Shi kuwa Alhaji tuni ya tafi gurun wani malami a ka ba shi maganin da zai raba tsakanin Bala da Babiya. Ya kuma samu nasara domin kuwa ya raba Bala da Babiya kuma ya auri Babiyar daga karshe.

Bala ya shiga damuwa matuka a lokacin da ya rasa Babiya, sai dai shi ma ya samu madadin soyayyar Babiya a gurun ‘yar kawunsa wato Fareeda (Hauwa M. Auwal). A sanadinta ne mahaifinta ya ba shi aron kudi don ya fara kasuwanci, wanda daga nan ne shi ma arzikinsa ya bunkasa, kuma har a ka yi aurensu da Fareeda. Sai dai a karshe kuma Alhaji Auwalu ya saki Babiya bayan wulkancin da ya yi a gareta.

 

Abubuwan Yabawa

  1. Sunan fim din ya yi dai-dai da labarin.
  2. Labarin bai yanke ba tun daga farko har karshen fim din.
  3. An yi amfani da kayan aiki mai kyau a fim din, saboda hotuna sun fita radau.
  4. Ba a samu sabani a tsakanin motsawar baki da fitar furuci ba, an samu daidaito a dukkanin fitowar.
  5. Fim din ya nuna tasirin soyayyar gaskiya da kuma rike amana.

 

Kurakurai

  1. Fassarar da a ka dora a cikin fim din wato (subtitle) ta na sabawa da abinda Jarumai su ke fada a gurare da yawa. Misali ‘yar uwar Babiya a na kiranta Habiba a cikin fim din amma, a na rubuta Hadiza a jikin fassarar.
  2. A lokacin da Bala da Fareeda su ka Babiya a wajen siyayya a bakin mota, an samu matsalar maimaici a wajen da a ka nuna Babiya ta shiga mota.
  3. Jera fitowa har guda hudu wadda ba a magana wato (non berbal scenes) ta yi yawa, za ta cirewa mai kallo karsashin kallon.
  4. Me ne ne hikimar nuno Bala da Babiya a kan babur, ba tare da an nuna daga ina su ke ko ina za su ba?

 

Karkarewa

Fim din Bala da Babiya ya nuna tasirin soyayyar gaskiya da kuma rike amana. Sannan ya samu nasarori a gurare daban-daban, duk da cewa ya dan samu ‘yan matsaloli marasa yawa. Fatanmu dai shi ne kara ingantawa domin a samu nasarar isar da sakonnin da a ke da burin isarwa ga masu kallo.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!