Connect with us

RAHOTANNI

USCOEGA: Tarihi Da Nasaorin Da Aka Samu A Tsawon Shekara Hudu

Published

on

An kirkiro kwalejin ilimin jihar Yobe: Umar Suleiman College Of Education da ke Gashuwa (USCOEGA), a lokacin tsohuwar jihar Borno a karkashin doka mai lamba 11, 1988; wadda kafin hakan tana matsayin ‘Adbanced Teacher’s College’.

A lokacin gwamnan mulkin soja, Laftanar Kanal Abdulmimini Aminu ne ya amince da bukatar sake kirkiro karin wasu kwalejojin ilimi guda uku a wasu manyan garuruwan jihar; Gashuwa, Biu da Bama, bisa ga yadda ake samun yawaitar gurabun karatu ga daliban da suka kammala makarantun sakandire.

A halin da ake ciki yanzu, wannan kwaleji: Suleiman College of Education, Gashuwa tana da manyan rassa guda uku- bangaren NCE, Digiri da Diploma.

Tun daga wancan lokacin, kwalejin take gudana a hannun hazikan shugabani (Probosts) masu kokari wajen ganin ta habaka tare da ci gaban ilimi a kasar nan; wadanda suka hada da Alhaji Ibrahim Gwio, Dr. Umar Mele, Alhaji Muhammad Gambo Bizi, Dr. Abba Daskum, Dr Muhammad Usman Dakasku, sai na yanzu; Dr Muhammad Gishiwa.

A daidai irin wannan zamani na ci gaban ilimin kimiyya da fasaha, da yunkurin Gwamna Mai Mala Buni na sake farfado da harkokin ilimi, Umar Suleiman College of Education tana bukatar haziki kuma kwararren shugaban wanda ya san makamar aiki daidai da kalubalen wannan zamani da sabuwar gwamnatin jihar Yobe, don bayar da gudumawar da za ta kai manufofin sabuwar gwamnati tudun mun-tsira, wajen bunkasa sha’anin ilimi, wanda kuma ko shakka babu, Dr. Muhammad Gishiwa ne ya dace da ita.

An nada Dr. Muhammad Gishiwa a matsayin shugaban (Probost) kwalejin ilimi ta jihar Yobe a ranar daya ga watan Junairun 2016, kuma tun daga wannan lokacin yake kokarin lalabo sahihan hanyoyin da zai bi don ciyar da ilimi a jihar gaba, ta hanyar bunkasa kwalejin- fiye da kowane lokaci.

Kuma a matsayin sa na kwararre kuma malami a makarantar, na tsawon sama da shekara 20, wanda hakan ya taimaka masa wajen fahimtar dimbin matsaloli tare da manyan kalubalen da makamantar ke fuskanta. Yayin da hakan ya tallafa masa wajen zakulo hazikan mutanen da zai yi aiki dasu su domin cimma nasarorin da ya sa gaba. Kuma samun wadannan nasarori da ya yi a cikin dan kankanen lokaci, ya nuna kasancewar sa zakakurin kwararren masanin halayyar dan Adam.

Dr Muhammad Gishiwa, jajirtaccen mutum ne wanda yake amfani da kwarewa tare da ilimin da Allah ya bashi, hadi da samun cikakken goyon bayan da gwamnatin jihar Yobe ke bashi tare da shawarwarin Mai Martaba Sarkin Bade (Alhaji Abubakar Umar Suleiman); sun dada masa kaimi wajen kai wa ga wadannan nasarorin da ya samu a cikin kankanen lokaci.

Dr Muhammad Gishiwa; mutum mai matsakaitan shekaru, an haife shi a Gashuwa ta karamar hukumar Bade, a jihar Yobe. Ya fara karatun sa na firamari a 1975, a makarantar Umar Suleiman Primary, a Gashuwa, inda ya kammala a Damagum Central Primary School. Daga nan ya zarce zuwa makarantar Gobernment Technical Secondary, da ke garin Damagum.

Malam Muhammad Gishiwa bai tsaya nan ba, ya tafi kwalejin horas da malamai ta jihar Borno; College of Education, Science and Technology da ke Bama- a 1987 zuwa 1989. Sannan ya zarce jami’ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar Borno, a 1989 zuwa 1992, inda ya samu digirin sa na farko a fannin ilimin addinin Musulunci mai zurfi (B.A  Ed: Islamic Studies).

A gefe guda kuma, tafiyar sa ta mika tare da samun cikar buri a rayuwa, wajen yi wa al’ummar kasa hidima da kokari wajen bayar da tashi gudumawa wajen raya harkokin ilimi, wanda bisa ga wannan kyakkywar niyya tashi, ya samu yabo daga gwamnatin jihar ta yaba da kwazon sa, ta bashi aikin koyarwa a Umar Suleiman College of Education, da ke Gashuwa a shekarar 1993.

A 2005, ya samu damar koma wa makaranta don karo ilimi, inda ya je jami’ar Bayeru dake Kano, domin digirin sa na biyu, a fannin ilimin yanayin halayyar dan Adam (M. Ed Psychology), wanda ya kammala da kyakkawan sakamako a 2010, sannan kuma daga baya ya koma BUK don yin digirin sa na uku (PhD) wanda ya kammala a 2018.

Dr. Muhammad Gishiwa, kwararre ne wanda ya kwashe sama da shekara 20 yana koyar da darussan ilimi a wannan kwalejin, kuma ya rike mukamai daban-daban, kuma tun a wancan lokacin yake da kyakkawar niyyar taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban bunkasa ilimi a jihar sa.

A lokacin sa ne kwalejin ta samu canje-canje masu ma’ana, tare da bude sabon baben farfado da sha’anin ilimin jihar Yobe. Yayin da shugaban makarantar ya yi amfani da matsayin sa wajen kyautata alakar kwalejin da takwarorinta a Nijeriya da ma a kasashen ketare- wajen musanyar bayanai da gudanar da binciken ilimi. Kuma a cikin wadannan shekaru hudu, ya yi aiki tukuru wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsaren da hukumomin kula ilimin manyan makarantun kasar nan (NCCE, NUC, TETFund, da makamantan su) suka shimfida don habaka sha’anin iIlimi.

Dr Gishiwa ya yi aiki a matsayin jekada nagari da kokari wajen ganin ya sauke nauyin da gwamnatin jihar Yobe, gwamnatin tarayya da iyayen dalibai suka damka masa, wajen samar da ingantaccen ilimin da Nijeriya da yan kasa za su dogara dashi don ci gaba, kyautata dabi’u, tarbiyya ta gari ga manyan gobe. Lamarin da ya jawo masa yabo daga hukumomin gudanar da harkokin ilimin manyan makarantu a kasar nan, da uwa-uba gwamnatocin jihar da a tarayya, shugabanin al’ummu da sauran su.

A bangaren kyautata jin dadin ma’aikata da karin samun horo ciki da wajen Nijeriya. A cikin shekaru hudu da ya yi a matsayin shugaban makarantar, Dr. Gishiwa ya yi fadi-tashin kyautata jin dadin ma’aikatan sa. A lokacin sa, kwalejin, ta hanyar hukumar TETFund, a cikin shekarar 2018, Malam Muhammad Gishiwa ya amince da tura malamai 68 zuwa karo ilimi; a jami’o’in Nijeriya da na kasashen ketare.

Daga cikin adadin, malamai 16 ne kwalejin ta dauki nauyin karatun digirin su na uku- a fannoni daban-daban, yayin da mutum 52 suka samu tallafin karatun digiri na biyu; ciki da wajen kasar nan. Kana da tura karin wasu ma’aikata 22 zuwa tarukan karawa juna-sani a kasashe daban-daban na duniya.

Dadin-dadawa kuma, ko a wannan shekara ta 2019, shugaban kwalejin ya rattaba hannu tare da amincewa da tura karin wasu malamai kimanin 48 don tafiya karo ilimi a jami’o’in Nijeriya da na kasashen ketare- mutum shida zuwa waje, inda 42 za su tsaya a gida Nijeriya. Sannan da tura karin wasu ma’aikatan ta 20, don halartar tarukan karawa juna-sani a kasashen duniya daban-daban.

A shekarun baya, wannan makaranta, ta sha fama da matsalar lalacewa da karancin dakunan kwanan dalibai, amma bisa jajircewar hukumar kwalejin, matsalar ta zama tarihi. A cikin wadannan shekaru hudu an gyara dakunan kwanan dalibai da gidajen bahaya, don ganin an samu kyakkawan yanayin da zai ba daliban sukuni da tsanaki a fannin karatu. Kuma an tona rijiyoyin tuka-tuka guda shida tare da na burtsatse guda biyu, don magance matsalolin karancin ruwan sha da na bukatun yau da kullum.

Hukumar wannan kwaleji, a karkashin Dr. Muhammad Gishiwa ta samar da makarantar sakandire don ma’aikatan kwalejin, domin kara bunkasa ilimi a matakin farko. Sannan kuma da farfado da bangaren sha’anin kiwon lafiya a kwalejin; ta hanyar sake gyara dakin shan magani wanda ya lalace kuma ba kayan aiki da magunguna. Inda yanzu aka samar masa da kayan aiki, ma’aikatan kiwon lafiya, domin su rika bayar da shawara da kula ga ma’aikata da daliban kwalejin a kananan matsalolin jinya.

A cikin shekaru hudu na shugabancin Dr. Gishiwa, hukumar kula da kwalejoji ta Nijeriya (NCCE) ta yi wa wasu karin kwasa-kwasan NCE 29 rijista, inda ita ma hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta amince da koyar da kwasa-kwasai 12 wadanda kwalejin za ta horas a matakin digiri.

Wasu karin nasarorin da Malam Muhammad Gishiwa ya samu a cikin wannan kankanen lokaci, ya yi kokari wajen bunkasa baki dayan dakunan gudanar da bincike a kwalejin; Physics, Chemistry, Biology, Animal Science, Soil Plant Science da sashen harsuna (Language Laboratory). Sannan da sake daidaita jarrabawar share-fage ga daliban NCE da Degree da hukumar tsara jarrabawar share-fage shiga jami’o’i ta kasa (UTME).

Da nasarori masu yawa wadanda ba za su lissafu a lokaci guda ba. Wannan yana daga cikin dalilan da suka jawo, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya saka sunan Dr. Muhammad Gishiwa a cikin yan kwamitin sake fasalin harkokin bunkasa ilimi, wanda ya kafa, jim kadan da hawan sa mulkin jihar.

Ko shakka babu, wannan hazikan kwararre ya cancanci yabo, sahoda yadda ya dauki dogon lokaci yana hidimta wa harkokin ilimi- tun daga tushe. Kuma mutum mai matukar kishin ci gaban al’ummar jihar Yobe da ma kasa baki daya. Ya dace gwamnatin jihar Yobe ta kalli irin wadannan kwararrun mutane (Dr. Muhammad Gishiwa), wajen amfani dasu wajen ci gaba da gina ilimi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: