Connect with us

Uncategorized

‘Yan Kurkuku Sun Yi Yunkurin Ballewa A Keffi

Published

on

An samu hatsaniya a kurkukun Keffi da ke jihar Nasarawa, ya yin da bursunoni sama da hamsin suka nemi ballewa daga kurkukun sakamakon rashin wadataccen abinci da rashin tsaftace muhalli.

Majiyar ta mu ta shaida mana cewa, dakyar ‘yan sanda  suka shawo kan masu zanga-zangar.

Majiyar ta ci gaba da cewa, baya ga rashin tsaftace nuhalli akwai karancin kula da lafiyarsu, wandanda suka sa ‘yan kukrkukun yunkurin ballewa daga cikin wannan kangin da suke ciki.

‘Yan kurkukun na fama da karancin ruwan shad a matsalar kazantar muhallin da suke ciki, sannanu kuma sun koka kan rashin samun bacci da daddare sakamakon cinkoson a cikin dakunan da suke kwana.

Haka kuma majiyarmu ta shaida mana cewa, tsananin wahalar da ‘yan kurkukun ke ciki ne ta su yunkurin ballewa.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar kula da bursuninin na jihar Nasarawa Mista Abene ya ce, yunkurin ballewar bursunonin ba sabon abu ba ne, da man wani lokacin ana samun hakan, sai dai ya ce, yanzu haka an kawo karshen wannan tawayen.

Sai kuma shugaban kurkukun, Mista Emmanuel Okoro ya karyata labarin cewa, ‘yan kurkukun sun yi yunkurin gudu ne. Ya ce, abin da ya faru shi ne wasu da aka hana shan taba ne a cikin kurkukun suka tayar da hatsaniya. Ba wanda ya gudu kuma ba wanda ya ji rauni.

Lokacin da ‘yan jarida suka isa gidan sarkin Keffi wanda kuma fadarsa ke kusa da kurkukun, Dakta Shehu Chindo Yamusa III ya tabbatar da afkuwar lamarin, sannan kuma ya ce, ‘yan sanda sun kwantar da tarzomar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: