Connect with us

KASASHEN WAJE

An Sake Samun Bullar Ebola A Congo

Published

on

Mahukunta a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, sun ce mutane biyu sun kamu cutar Ebola a yankin Kudancin Kibu, wanda shi ne karo na farko da aka samu wadanda ke dauke da kwayoyin wannan cuta, yayin da tuni daya ya mutu.

Mataimakin sakataren yada labarai a fadar shugaban kasar ta Congo, Giscard Koussema, wanda kuma mamba ne a kwamitin yaki da wannan annoba a kasar, ya tabbatar da wannan al’amari, inda ya ce wata mata da kuma danta da suka fito daga garin Beni ne a arewacin Kibu suka kamu da cutar.

Ya ce, a halin da ake ciki, jami’an kiwon lafiya sun killace wannan yanki, sannan ana ci gaba da aikin tantance wadanda suka yi cudanya da wadannan mutane biyu.

Yanzu haka daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar wanda ke raye, na karkashin kulawar jami’an kiwon lafiya.

To, sai dai birin Bukabu mai tazarar kilomita 500 daga inda aka samu bullar annobar yana fuskantar barazana, amma dai ana ci gaba da sa-ido sosai dangane da jama’ar da ke shiga yankin na Kudancin Kibu.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: