Connect with us

RAHOTANNI

Dalilin Da Ya Sa Aka Garkame Kasuwar Sayar Da Dabbobi Ta  Enugu

Published

on

Shuwagabannin kungiyar kasuwar sayar da dabbobin gida da kayayan  gwari na Arewacin Nijeriya tare da kungiyar Miyyatti Allah ta Nijeriya sun  yanke shawarar haramtawa makiyayan da ba su zaune da iyalinsu a Jihohin Kudu-maso-gabas kasar yin kiwon dabbobi a fadin yankin.

Shugaban kungiyar ta yankin Kudu-maso-gabashin kasa Gidado Siddiki ya sanarwa da manema labarai hakan jim kadan bayan taron da suka gudanar a jihar Enugu.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen bankado dukkanin ayyukan ta’addanci a Jihar. Shugabanin sun kuma bayyana rufe kasuwanni hudu na sayar da dabbobi da kayan gwari a Jihar ta Enugu daga ranar Laraba mai zuwa ranar Alhamis domin samun damar gudanar da wani yawon wayar da kai a kasuwanni da kuma wasu mazaunin Fulani makiyaya sha hudu da ke  Jihar.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: