Connect with us

MAKALAR YAU

Illar Shaye-Shaye Ga Matasanmu

Published

on

Na taba yin rubutu sau biyu dangane da shaye shaye, na farko na yi ne a kan shahararren attajiri kuma matashin mawakin nan na kasar Amurka mai suna Lil Wayne, wanda shaye shaye ya sauya tarihin rayuwarsa gabaki daya, rubutun mai taken ‘Illolin shaye shaye ga matasa, darussa daga rayuwar Lil Wayne’ ya fara fita ne a tsohuwar mujallarmu mai suna ‘Matasa’.

Sai kuma na biyu a kan yadda shaye shayen magungunan Mura ya zama ruwan dare a arewacin kasarmu Nijeriya, musamman ma yadda Mata ke tsunduma cikin harkar ba kakkautawa. Shi ma wannan rubutun na yi shi ne a mujallar Matasan; bugu na hudu da bugu na Shida.

Rubutun farko wanda na dirarwa mawaki Lil Wayne, na bayyanawa masu karatu irin mummunan halin da shaye shaye ya jefa wannan attajirin matashi da kuma yadda shan miyagun kwayoyi da hodar iblis su ka zama sanadin mutuwar shakikinsa mai suna Static Major.

Wata yarinya ta yi min martani ta wayar salula ta na kare Lil Wayne, bisa hujjojin cewa wai muna batawa mawaka suna ne a fakaice wanda yin hakan kuma bai dace ba, sannan kuma idan labarin ya iya riskarsa (Lil wayne) zai rika kallon Nijeriya a matsayin kasar da a ke kiyayya da shi. Ko da ta kashe wayar, na sha dariya har sai da cikina ya yi fal.

A rubutu na biyu kuma, wanda na yi wa maudu’i da ‘Tutolin, Parkalin, Emzolyn’, wasu mashayan samari ne da ke unguwar da na ke zaune su ka same ni cikin izgili (duk da na sansu) su ka ce, sun ga rubutu, an yi kokari don Allah su na jiran kashi na biyu, ko yaushe zai fito?

A wannan karon, na sake bayyana ne da sabon bincike a kan yadda shagunan sayar da magunguna (kemis) su ka koma sansanin sayar da kwayoyi da kayan maye. Idan a shekarun baya, sai an wahala kafin a samu tabar wiwi ko Sholisho, yau sai dai kawai ka je shagon Kemis ka bukaci maganin mura.

Me a ke nufi da shaye shaye?

Wannan tambaya idan a ka yi wa mutane 10 ita, zai yi wahala a samu amsa iri guda daga kowanne daya daga cikinsu. Amma dai, kowanne zai yarda da cewa shaye shaye shi ne kurewa magani geji, ko shan abin da ba an yi sa ba ne don amfanin kwakwalwar dan Adam.

Da yawan matasan da ke shaye shaye, su na fadawa tafarkin ne saboda dalilai daban daban. Wadanda su ka dauki dabi’ar a makaranta, sun kwaikwaya ne a wurin abokan da su ke hulda da su. Wannan ni shaida ne ga daliban da na san ko magana ba su yi sosai, amma wani abin mamaki, cikin shekaru biyu sai na ji sunayensu cikin gawurtattun ‘yan wiwin makarantar da na yi sakandare.

Daga bisani sai ta bayyana cewa abokan da su ke mu’amala da su, su ne su ka koya masu wannan halin. Akwai wadanda kuma ba su je makarantar boko ba, don haka su ba a can su ka koyi shaye shaye ba. Irin wadannan su ne a ke kira ‘yan tasha. A shekarun baya, shaye shaye da rashin mutunci an fi tsammaninsu a wurin ‘yan tasha.

Har yanzu, idan a na son cin mutuncin mutum sai a kira shi da sunan dan tasha. Ba abin mamaki ba ne don an samu dan tasha da halayyar shaye shaye, saboda dabi’ar rayuwarshi a tasha sun hada da rashin dattako, cije – cije, da sauransu. Idan wata diya ta yi mursisi ta sha, to menene dangantakar diyar malam Bahaushe da shaye shaye?.

Wani ba zai yarda ba, amma ni na san ‘yan matan hausawan da su ke shan wiwi fiye da maza, kuma kwakwalwarsu ta na dauka caraf, wuce tsammani. Akwai wacce ma idan ta matsa sholisha a dankwalinta, sai a hankali.

Bude kemis birjik, ba tare da bin ka’idoji ba shi ne ya fara kawo cikas ga kula da kiyaye harkar magunguna. Kamar yadda mutum zai bushi iska ya bude shagon sayar da kayan ci da sha, ko kayan sayar da bulawus da kayan kwalliya.

Haka nan yanzu a ke busar iska a bude kemis a Nijeriya. Da ma bude Kemis din ne kawai, da sai mu ce da dan sauki, amma ba a nan abin haushin ya tsaya ba, wanda zai kula da shagon (mai sayar da kaya), sai ka ga wani bai taba shiga makaranta ba, ballantana ya san wanne kwaya da wacce kwaye a ke sha idan ciwon kai ya addabi mutum, ko cikinsa ya kulle.

Don haka, idan ma da gaske ne hukumomin yaki da shaye shayen miyagun kwayoyi su na aikinsu na son kawo cikas ga shan abubuwan da ke sa maye. To wajibi ne su fara da tsafta ce kemis – kemis din da a ka bube su ba tare da bin ka’ida ba.

Da yawan matasa, mata da maza sun dauki dabi’ar yi wa maganin Tari da Mura shan wuce lissafi ne saboda yadda su ke son sauya rayuwarsu zuwa irinta mawakan kasar Amurka, ko kuma su yi rayuwa irin ta abokai ko makusanta.

Shi dai ka barshi ya yiwa abokan tambelensa zarra, idan ya yi magana sai ka ji muryar kamar an tsaga ganga. Har ma a rinka kiranshi kwaro, saboda idan ya zauna a gaban kemis, sai ya sha kwalba hudu zuwa biyar.

Matasanmu masu wadannan ‘yan shaye shaye sun kasa gane cewa, shi fa mawaki Lil Wayne, Wiz Khalifa, D.J Khalid ko Birdman din da su ke kwaikwayo, ba su na sha ba ne alhali su na zaune banza ba su maganin sisi. Attajirai ne na gaske wadanda su ka samu kudadensu ta hanyar fasa banki, safarar hodar iblis, amma duk da haka shaye shayen bai zama alheri a wurinsu ba.

Ku kuma kuna nan Nijeriya, ba ku tunanin yadda za a yi a daina murgude zabe, ba ku tunanin yadda za a magance matsalar tsaro, ba ku tunanin yadda za a gyara tituna da wutar lantarki, ba ku tunanin yadda talauci zai yi sauki a cikin al’umma, sai dai koyi da wani katon Ba’amurken da bai san hagunsa ba balle dama. mu hadu mako mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: