Connect with us

KASASHEN WAJE

Indonesiya Za Ta Sauya Babban Birnin Kasar

Published

on

Shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo ya mikawa zauren majalisar dokokin kasar bukatar canza babban birnin kasar daga Jakarta zuwa Kalimantan da ke tsibirin Borneo.
Wannan bukata na kunshe cikin jawabin da shugaban ya gabatar a majalisar, cikin shagulgulan cikar kasar shekaru 74 da samun ‘yanci kai. Joko Widodo zai sake karbar rantsuwar wa’adi na biyu a shugabancin kasar cikin watan Oktobar bana, sakamakon nasarar sake lashe zabe da ya yi.
Shugaban ya bayyana tattalin arziki da daidaito da kuma adalci a matsayin ma’aunin dubawa, idan ana batun babban birni ko fadar mulkin kowacce kasa.
Don haka ya mika takatardar sauya mazaunin gwamnati daga Jakarta, izuwa Kalimantan da ke tsibirin Borneo.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: