Connect with us

WASANNI

Modric Na Neman Afuwar Magoya Bayan Real Madrid

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Luca Modric, ya bayyana nadamarsa a fili bayan da a ka ba shi jan kati a wasan da kungiyarsa ta lallasa Celta Vigo daci 3-1 a gasar laliga.

An bashi jan katin ne bayan ya daki dan wasa Dani Suares na Celta Vigo a lokacin ana buga 1-0 a wasan sai dai daga baya dan wasan ya bayyana cewa ba halinsa bane dukan ‘yan wasa kuma tsautsayi ne yasa hakan ta kasance a kansa.

A ranar Asabar Real Madrid ta buga wasan farko na laliga da kungiyar kwallon kaf ata Celta Vigo kuma ta zazzaga kwallaye uku a ragar Celta Vigo yayinda aka zura musu kwallo guda daya dab da za’a tashi daga wasan.

“An bani ja  kati bisa kuskure saboda bani da burin taka dan uwana dan wasa kuma tsautsayi ne ya faru a kaina saboda haka bana fatan zai sake faruwa anan gaba kuma ina neman afuwar magoya baya da kuma dan wasa Suares” in ji Modric wanda shine gwarzon dan kwallon duniya na yanzu.

Shima Kaftin din Real Madrid ya bayyana cewa tabbas Modric baiyi niyyar dukan Suares ba wanda har zao kai a bashi jan kati amma tun da na’urar taimakawa alkalin wasa ta tabbatar da cewa yayi laifi babu matsala saboda babban burinsu shine kare kowanne dan kwallo.

Kawo yanzu Real Madrid zata sake buga wasa na biyu da kungiyar kwallon kafa ta Balladolid a kokarin da kungiyar takeyi na ganin ta lashe gasar laliga ta wannan shekarar da gasar cin kofin zakarun turai.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: