Connect with us

TARIHI

Rayuwar Sayyadina Ali Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci (IV)

Published

on

Yau ma cikin yardar Allah zamuci gaba a inda muka tsaya a makon daya gabata.

Mu tsaya ne a inda muka ce, Al’amarin da Rabbus Samawati ya hukunta ba wurin kauce masa. Don haka sai Dalhah da Zubairu suka hana Uwar Muminia Nana Aisha Radiyallahu Anha komawa, suka ce da ita, ba ruwanki da yaki, abin da muke so kawai shi ne, ‘ya’yanki Musulmai su gan ki, su san kina da goyon bayan wannan lamari don su samu kuzarin ba da himma a cikinsa.

Uwar Muminia Nana Aisha Radiyallahu Anha sam bata gamsu da haka ba. Bayan da aka kare yakin basasar rakumi, Sayyadina Ali ya aika wani Manzo mai suna Abu Muslim al Khaulani domin ya jawo hankalin Mu’awiyah a kan hadewa da sauran al’ummar Musulmai wadanda su kayi mubaya’a.

Amma ga alama wannan karon Mu’awiyah ya fi tsananin cijewa ma fiye da in da aka fito. Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya sake aika shahararren Sahabin nan Nu’uman dan Bashir, shi ma dai bai ci nasara ba. Daga nan ne Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya yanke shawarar yakarsa.

Ya fara tura runduna wadda ta kunshi mayaka kimanin 6000 zuwa 7000 karkashin jagorancin Ashtar An Nakha’i domin su fara kai farmaki a kansa. Kafin Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya aike da rundunarsa kuwa, sai da ya jinjina karfin Mu’awiyah da jama’arsa. Hanyar da ya bi wajen gano karfin Mu’awiyah ita ce, ya aika wani mutum wanda ya nuna alamun shi matafiyi ne daga Iraki yana mai sanar da Mu’awiyah cewa, ga Sayyadina Ali nan tafe da rundunarsa zai yake ku.

Da Mu’awiyah ya ji wannan labara, sai ya sa aka tara dukkan mutanen Sham in da ya yi huduba yana neman shawarar jama’a game da matakin da za a dauka, amma ba wanda ya daga kansa sama ko ya ce uffan saboda biyayya. Daga bisani wani mutum da ake kira Zul kila’i ya kada baki ya ce masa, kai ne mai yanke hukunci, mu namu shi ne zartarwa. Dan aiken Ali ya garzaya ya fado masa abinda ya gani. Amma dai Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam bai karaya ya fasa abinda ya yi niyya ba.

Bayan da Mu’awiyah ya hakikance Sayyadina Ali ya fito da rundunarsa, sai shi kuma ya shirya tasa runduna mai irin yawan waccan, ya kuma fito domin karawa da su. Amru dan Ass ya kawo masa gudunmawa a dai-dai wani ruwan tafki da ake kira Siffin. A kan wannan ruwan ne ma aka dan samu gumuzu kafin hankali ya kwanta a soma tattaunawa tsakanin wakilan Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam da na Mu’awiyah, har a cimma yarjejeniyar yin amfani da ruwan tare da juna.

Da ya ke Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya gano muhimmancin mutanen kufa a yakin da aka yi a baya, ya aika Manzo na musamman wanda shi ne Hashimu dan Utbata dan Abu wakkasi don ya sake nema masa goyon bayansu ta hanyar gwamnansu Abu Musa Al Ash’ari.

Shi kuwa Abu Musa kamar yadda muka fada a baya, yana daga cikin masu ra’ayin farko na ganin bai cancanta ayi yakin ba. Wannan kuwa shi ya janyo Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya tube shi daga kujerarsa, ya nada Kurazah dan Malik a madadinsa. Sannan ya sanya Ammar ya je ya janyo hankalin mutane don su ba da goyon baya.

Ya kuma nemi dansa Alhussan da ya rufa masa baya. Alhussan kuwa ya yi da’a ga mahaifinsa. Mutanen kufa kuwa sun amsa wannan kira na Sarkin Musulmai domin sama da mutane dubu goma sha biyu ne suka fita don mara masa baya. Ammar ya ci gaba da bayar da goyon bayansa ga Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam har ajalinsa ya cim masa a hannun daya daga cikin mutanen Mu’awiyah.

Babu shakka kuwa mutuwarsa tasa Mu’awiyah da jama’arsa cikin bala’I da masifa. Domin kuwa da yawansu (musamman ma dai Sahabbai daga cikinsu) sun canza sheka daga wajen Mu’awiyah suka koma bangaren Sayyadina Ali saboda la’akari da wani sanannen hadisi a tsakaninsu wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake cewa, Ammar zai gamu da ajalinsa a hannun wata kungiya mai kira izuwa ga wutar jahannama. (Sahihul Bukhari littafin Sallah, Babin taimako a Masallaci Hadisi na 447).

Ra’ayin Sahabbai Dangane da wannan yakin: Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun kasu kashi uku dangane da wannan yakin. Kashi na farko su ne wadanda su ke da ra’ayin cewa, yakin bai ma dace ba gaba daya. Kuma kan al’umma ya wajaba ya hadu a wuri daya maimakon yaki a tsakanin junansu.

Irin wadannan bayin Allan sun yarda da khalifancin Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam kuma sun yi masa mubaya’a, amma dai yakin ne ba su aminta da aukuwarsa ba. Wadannan su ne akasarin Sahabbai, a cikinsu har da Sa’adu dan Abu Wakkas da Muhammadu dan Maslamah da Abdullahi dan Umar bin khattabi da Abu Musa al Ash’ari (Gwamnan Kufa) da Abu Bakrata Al thakafi da Abu Mas’ud al Ansari da makamantansu.

Hujjojin wadannan bayin Allan suna da dama, kuma sun hada da duk hadissan da ke magana a kan barin yaki lokacin fitina. A cikinsu ma har da wadanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi alkawari da su cewa, duk halin da aka shiga kar su yi yaki da Musulmai. (Sahihul Bukhari kitabul Fitan (8/95), da Sunan Al Tirmizi Kitabul fitan (3/332), da kuma Musnad na Ahmad (4/225))

Kashi na biyu kuwa, suna ganin cewa, tun da ya ke Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam shi ne nadadden Sarkin Musulmai, wanda ya wajaba a yi wa biyayya, wajibi ne a yaki dukkan wanda ya fandare ma sa. A kan haka suna yaki tare da shi a kan Mu’awiyah da jama’arsa. Suna kuma kafa hujja da dalillai na Alkur’ani da hadisi masu nuna wajabcin biyayya ga shugabanni.

Daga cikin wadanda suka dauki wannan matsayin har da fitattun Sahabbai irin su Abdullahi dan Abbas da Ash’as dan kais da Ammaru dan Yasir Radiyallahu da Maliku dan Ka’abu al Hamdani da dai sauransu. Ga wata tattaunawa da ta gudana a tsakanin Ammaru da Abu Mas’ud al Ansari Radiyallahu Anhuma (daga cikin masu ra’ayin farko na kauracewa yakin) a kan wannan mabanbancin ra’ayin nasu, Buhari ya ruwaito ta kamar haka:

Abu Mas’ud ya ce: Ya kai Ammar! Ka sani duk a cikin tsaranka babu wanda ya kai matsayinka a wurina. Kuma ba ka taba sanya kanka a cikin wani lamari ba wanda yake aibanta ka a wurina sai gaggawar da kake yi a cikin wannan fitina.

Ammaru ya ce da shi: Ya kai Baban Mas’ud! Ni kuma wallahi ba ka da wani aibi a gurina kai da abokinka (Amru dan Ass) wanda yake aibata ku tun bayan rasuwar Manzon Allah kamar janye jikinku daga wannan lamari (yana nufin taimaka wa Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam).

A yayin da kashi na uku na Sahabbai su ko su ke ganin cewa, Mu’awiyah ne yake da hakkin ya nemi fansar jinin dan uwansa khalifa Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu, kuma dole ne a taimaka masa don ya cimma biyan wannan bukata. Suna kafa hujja da ayar Suratul Isra’i wadda Allah a cikinta yake cewa,

Wanda duk aka kashe shi a kan zalunci to, hakika mun sanya hujja ga waliyyinsa (a kan ya nemi fansa), sai dai kar ya wuce iyaka a wajen kisan (ramuwa), domin lalle shi abin taimakawa ne. (Suratul Isra’i, Aya ta 33). Haka kuma suna kafa hujja da hadissan da suka bayyana cewa, fitina zata auku, kuma idan ta auku Usman shi yake a kan gaskiya tare da mutanensa. Sai suna ganin su ne mutanen Usman tun da su ke fada dominsa.

Daga cikin masu wannan ra’ayi akwai Sahabbai kamar Amru dan Ass da Ubadata dan Samitu da Abud Darda’I da Abu Umamata al Bahili da Amru dan Ambasata da dai sauransu.

Idan muka yi la’akari da hadisin da Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, A yi bushara ga duk wanda ya kashe Zubairu da wuta, da hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma Dalhah bushara da zai yi shahada za mu gane cewa, wadansu suna da uzuri a yakar Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam da sukayi. Domin kuwa dama ba shi suka zo yaka ba.

Mu’awiyah yaki yayiwa Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam mubaya’a, saboda wai sai anbashi makasan Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu ya kashe saboda hakinsa ne, domin shi dan uwan Sayyadina Usmanu ne. Shi kuma Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam na cewa, in kana son haka, ka amince da shugabancin da aka nada tukuna, sai ka kawo kara ga gwamnati ta bincika tayi hukunci. Mu’awiyah na nan a kan bakarsa, ni ba zan yi ma ka mubaya’ah ba in dai har ba za ka iya daukar fansar wanda ya gabace ka ba, kuma ba za ka ba ni dama ni da ni ke da hakki ba. (Mukaddima, na Dan Khludun (1/257)).

Za mu dakata a nan, a mako mai zuwa insha Allahu za mu kammala wannan tarihin na babban gwarzon musulunci, wato Sayyadina Ali dan Abu Dalib Alaihi Salatu Wassalam. Sannan kuma muna sanar da ‘yan uwa cewa zamu sake zaban daya daga cikin khalifofin Annabi Sallalahu Alaihi Wasalam mu bada tarihin rayuwarsa da ayyukan yada addinsa domin ‘yan uwa su amfani da shi.

Daga dan ‘yarwarku,

Mohammed Bala Garba, Maiduguri.

08098331260
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: