Connect with us

WASANNI

Real Madrid Za Ta Yi Wa Pogba Tayin Karshe

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Sipaniya sun ruwaito cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata kai tayin karshe ga Manchester United domin daular dan wasan tsakiyar kungiyar, Paul Pogba, wanda shima yakeson komawa kungiyar da buga wasa.

Wakilin dan wasan dai yana nan yana kokarin ganin dan wasan ya koma Real Madrid saboda yana fatan ganin yabar kasar Ingila sai dai Manchester United tayi alkawarin zatayi watsi da duk wani tayi da za’a kawo akan dan wasan tsakiyar nata.

Tun bayan daya karbi aikin koyar da Real Madrid, kociyan kungiyar, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa yana fatan kungiyar zata sayo masa dan wasa Paul Pogba da kuma Edin Hazard sai dai Hazard din kawai aka iya kawo masa.

Shugaban kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez, yana nan yana kokarin ganin ya sayo dan wasa Neymar sai dai Neymar din kuma yafi son komawa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona wadda yabari shekaru biyu da syka gabata.

Real Madrid dai tayi kokarin ganin ta sayarwa da Bayern Munchen dan wasa Gareth Bale sai dai ita kuma Munich din tafi son dan wasa Coutinho wanda tuni har ya kammala komawa kungiyar a matsayin aro.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa mai koyarwa Zidane yayi barazanar barin aikin Real Madrid idan har kungiyar bata sayo masa Pogba ba wanda yace yana fatan zai gina kungiyarsa da dan wasan dan kasar Faransa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!