Connect with us

RAHOTANNI

Sarkin Bichi Da Na Rano Sun Kai Wa Gwamnan Kano Gaisuwar Sallah

Published

on

Mai Martaba, Sarkin Bichi, Alhaji Dakta Aminu Ado Bayero, ya kai wa Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahu Umar Ganduje, ziyarar Sallah tare da daukacin Hakimai da kuma sauran manya-manyan ‘Yan  Majalisarsa, zuwa Fadar Gwamnatin Jihar Kano.

Haka zalika, Sarkin Bichin, ya samu tarbar Mai girma Gwamna, tare da Mataimakinsa Dakta Nasir Yusuf Gawuna, da kuma sauran manya-manyan jiga-jigan Gwamnatin Jihar Kano, ciki har da Mai girma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon. Alhaji Abdullahi Abbas (Dan Sarki, Jikan Sarki), a ranar Juma’ar da ta gabata.

A bangare guda kuma, shi ma takwaran Sarkin na Bichi, Mai Martaba Sarkin Rano, Dakta Tafida Abubakar 11, Autan Bawo, ya kai irin wannan ziyara ta Sallah, tare da girmamawa ga Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a Fadarsa da ke gidan Gwamnatin Kano.

Har ila yau, shi ma ya samu irin waccan kyakkyawar tarba ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da Mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusif Gawuna, da kuma sauran manya-manyan makarraban Gwamnatin Jihar.

Wakazalika, kafin zuwan wadannan Sarakuna masu daraja ta daya, wannan ziyara tare da taya Mai girma Gwamna murnar Sallah, shi ma Sarkin Karaye, Alhaji Dakta Abubuakar II, ya ziyarci Fadar Gwamnatin Jihar Kano, domin yi wa Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, murnar Sallah tare da yi masa fatan alhairi da kuma addu’ar Allah Ya maimaita mana ganin ta badin-badada.

A cigaba da mai girma Gwamna yakeyi na karbar gaishe gaishen Sallah daga masu girma Sarakunan Kano masu Daraja ta daya a fadarsa dake gidan Gwamnatin jihar Kano

Allah ya Taimaki sarki ya kara wa Sarki lafiya ya taimaki Gwamnatin jihar Kano tare da Mukarrabanta baki daya Amin

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: