Connect with us

RAHOTANNI

Sarkin Fika Ya Yi Kira Ga Jama’a Su Guji Zuba Shara A Magudanun Ruwa

Published

on

Shugaban majalisar sarakunan jihar Yobe, kuma Sarkin Fika, Mai Martaba Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, ya gargadi al’ummar jihar Yobe kan cewa su guji zuba shara a magudanun ruwa tare da kiyaye gina gidaje a hanyoyin ruwa, don kaucewa barkewar ambaliyar ruwa a jihar.

Sarkin Fika ya yi wannan kiran, ta bakin mai taimaka masa ta fuskar yada labarai- Alhaji Mohammed Abubakar, inda ya kara da cewa, ta yadda ake samun ruwan sama masu karfi a daminar bana, yar manuniya ce ga jama’a kan su guji aikata hakan.

“Kuma a matsayin mu da yan Adam, akwai bukatar mu yi amfani da wannan muhimmiyar dama ta ni’imar da Allah ya taskace a lokacin daminar don yin noma tare da addu’o’in samun kaka mai albarka”. Shawarar Mai Martaba.

Bugu da kari kuma, Shugaban majalisar sarakunan ya yi kira na musamman ga iyaye kan cewa su rinka kula da yanayin halayen ya’yan su, a cikin kowane lokaci kuma ya yi kira na bai-daya ga jama’ar jihar Yobe da su ci gaba da zaman lafiya tare da junan su, duk da bambancin addini da al’adu.

“Ina mai farin-cikin kara nanata muku cewa ku hada kai kuma kowa ya zauna lafiya da dan uwan sa. Kuma muna bayar da shawara kan ku bayar da rahoton duk wasu take-taken tashin-tashina da baku lamunta dasu zuwa ga jami’an tsaro kuma ku kasance masu dausasa harsunan su tare da dukufa da addu’o’in samun kaka mai albarka, a wannan damina ta bana”. In ji shi.

A karshe, Mai Martaba Sarkin Fika, ya bukaci al’umma da su bai wa gwamnatin cikakken goyon baya bisa kyakkawan manufofin ta da tsare-tsaren ta, wanda ta haka ne zai basu damar amfana da romon dimukuradiyya.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: