Connect with us

RAHOTANNI

Sarkin Kano Ya Samu Sabon Mukami Daga Kasar Kanada

Published

on

A ranar Talatan da ta gabata, wata Kungiya mai ba da damar samun ilmi mai inganci ga Malaman makarantu a ko’ina a fadin duniya (1Million Teachers Inc) da ke Kasar Kanada, ta nada Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a matsayin Shugaban kwamatin bayar da Shawara a Nijeriya.

Haka zalika, Kungiyar ta ayyana Sarkin Kanon a matsayin mamba na kwamatin Uwar wannan Kungiya da sharkwatarta ke can Kasar ta Kanada.

Har ila yau, kamar yadda wannan Kungiya ta bayar da sanarwa a wannan mako da muke ciki, ta bayyana Kungiyar a matsayin wadda ke bayar da damar samun ilmi mai inganci ga Malaman makarantu daban-daban a ko’ina suke kuwa a fadin duniya baki daya, musamman wadanda ke zaune a wuraren da babu sukunin samun wannan ingantaccen ilmi.

Wakazalika, majiyarmu ta samu sanarwar cewa, Babban Daraktan Kungiyar, Hakeem Subair, ya bayyana matukar farin cikinsa game da wannan nadi da aka yi wa Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi 11.

Kazalika, Babban Sakataren ya kara da cewa, Ko shakka babu, wannan babban abin karfafa gwiwa ne ga wannan kungiya tamu. Dalili kuwa, wannan Kungiya mai ba da damar samun ilmi mai inganci ga Malaman makarantu (1Million Teachers Inc).

“A kodayaushe, muna neman jagorori tare da muryoyi masu ƙarfin gaske, domin su taimaka mana wajen ci-gaba da yada manufofinmu da kuma sauran kudirorin da muke san cimma a wannan bangare, domin samun damar samar da ingantaccen ilmi ga kowa da kowa, musamman mata masu tasowa, sannan da bayar da shawarwari ga wannan kungiya tamu”, in ji shi.

Haka nan, muna sake bayyana matukar farin cikinmu tare da yin maraba da lale ga Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, CON, a matsayin Shugaban Kwamatin Mai ba da shawara na wannan Kungiya mai bayar da damar samun ilmi mai inganci ga Malaman makarantu a ko’ina a fadin duniya (1Million Teachers Inc), a cewar Babban Sakataren.

Sanarwa ta kuma ce, Shugaban kasa Muhammadu Buharu ya ce, “An kafa wanna rundunar na musamman ne don tabbatar da zaman lafiya a yakin arewa maso yammacin kasar nan da ma kasar baki daya.

“A matsayina na shugaban dakarun Nijeriya ina da tabbacin za ku iya gabatar da ayyukan da aka dora muku na kawo zaman lafiya a kasar nan, ina kuma da imanin za ku iya.

“Ina tsammanin ba zaku bar wani dan ta’adda ko daya ba, ku gano tare da kashe su a duk inda kuka gan su gaba daya.

Shugaban wanda ya samu rakiyar Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya tabbatar wa da sojojin cewa, gwamnantinsa za ta yi dukkan abin da ya kamata na ganin an kawo karshen yan ta’adda a fadin kasar nan tare da samar da dawamammen zaman lafiya gaba daya.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: