Connect with us

KASASHEN WAJE

‘Yan Adawa Sun Sha Dukan Tsiya A Zimbabuwe

Published

on

‘Yan sandan kwantar da tarzoma a Zimbabuwe, sun yi dirar mikiya a kan ‘yan adawa da ke zanga-zanga, duk da dokar haramci da gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta gabatar

Masu gangamin na zargin gwamnatin mai ci da zaluncin da ya shige na hambararriyar gwamnatin Robert Mugabe da ta gabata.

‘Yan adawar dai sun yi gangami a dandalin taro da ke birnin Harare, domin kokawa da halin kaka-ni-ka yi da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Tun da farko kotun kasar ta haramta gudanar da gangamin, a yayin da aka girke jami’an tsaro a sassa daban-daban na babban birnin Zimbabuwe.

Sai dai babbar jam’iyyar adawar kasar ta yi kira ga mayo bayanta dasu kauracewa gangamin, saboda gudun zubar da jini.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: