Connect with us

RIGAR 'YANCI

Yanzu Muka Fara Gwagwamaryar Kwato Hakkkin Al’ummar Kano Da Aka Yi Wa Kwace -Falaki

Published

on

Hadaddiyar Muryar Malaman Kwankwasiyya ta kasa ta bayyana aniyarta na ci gaba da gwagwamaryar fatan ganin an dawowa da Kanawa zaben da aka yi masu fyadensa a lokacin zaben gwamna da ya gabata, jawabin haka ya fito daga bakin shugaban Kungiyar Muryar Malam Kwankwasiyya na Kasa Sheikh Gwani Musa Falaki Tsakuwa alokacin khatamar saukokin alkur’ani da ya jagoranta a kwanaki goma na watan Zulhajji.

Sheikh Falaki ya bayyana cewa al’ummar duniya sun zuba ido kan kotun sauraron korafe-korafen zabe da ke zamanta a Kano, domin ganin yadda za ta kasance musamamn idan aka yi la’akari da abubuwan da suka bayyana a lokacin wancan zaben da Jam’iyyar APC ke ikirarin lashewa a cewarsu, amma dai ko wanda bai taba ganin yadda ake zabe ba ya san Jam’iyyarmu ta PDP karkashin jagorancin dan kishin kasa da al’ummarta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta ya san Abba Kabir ne ya lashe zaben.

Hakazalika Malam Musa Falaki ya yi amfani da wannan dama domin mika sakon taya murna ga al’ummar Muslmu a duk inda suke a duniya bisa samu damar gudanar bukuwan sallah tare da yiwa alhazammu fatan Allah ya dawo mana da su gida lafiya. Haka kuma Gwani Falaki ya tabbatar da cewa yanzu haka sun kara zage damtse wajen amfani da wani gagarumin taron addu’a da za a gudanar domin fatan Allah ya bai wa Abba Nasara a shari’ar da ake da wadanda ke kokarin yi wa Kanawa fashin zaben da suka yi wa abin da suke so kuma suke da kyakkyawan yakinin  shi ne alhairi ga ci gaban Kano da Kanawa.

Da aka tambaye shi kan batun shaidun da jam’iyyarsa ke ta kokarin ba ta damar gabatarwa, sai ya amsa da cewa ina tabbatar maka da cewa razana suka yi da wadannan shaidu, shi ne daliln da ya sa suke ta fakamniya, wanda kuma shue shure  ba zai hana mutuwa ba, yanzu haka muna da yakinin cewa Jam’iyyar APC duk sun firgice da irin yadda jama’a suka damu kwarai tare da fatan samun cikakkiyar nasarar damka kujerar Gwamna ga halsataccen zababben gwamna Abba Kabir.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: