Connect with us

KASASHEN WAJE

‘Yar Majalisar Amurka Ta Yi Watsi Da Tayin Isra’ila

Published

on

‘Yar majalisar wakilan Amurka, Rashida Tlaib, ta yi watsi da tayin gwamnatin Isra’ila na bata damar shiga kasar domin ziyartar mahaifiyarta dake yankin yamma da kogin Jordan.

Tlaib ta bayyana sharuddan da Isra’ila ta gindaya mata kafin shiga kasar, a matsayin tauye hakki, abin kunya da kuma takaici.

A ranar Alhamis Isra’ila ta hana Ilhan Oumar da Rashida Tlaib ‘yan majalisar wakilan Amurka na farko mata Musulmi, shiga cikinta, saboda ficen da suka yi wajen sukar matakan da take dauka kan Falasdinawa.

Sai dai ranar Juma’a Isra’ilar ta baiwa Tlaib damar, bayan gindaya sharuddan cewa ba za ta yi magana kan hakkokin Falasdinawa da gwamnatin Isra’ila ba, kuma tilas ta kaucewa duk wani al’amari na siyasa, inda ita kuwa ta ce sam hakan ya saba wa hakkin dan adamta, tana mai shure sharuddan.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: