Connect with us

RIGAR 'YANCI

Zaben 2023: Shugaba Buhari Ba Zai Iya Dorawa ‘Yan Nijeriya Mutumin Da Ba Su So Ba In ji Shugaban Majalisar Nasarawa

Published

on

Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi, Shugaban Majalisar Jihar Nasarawa ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulkar Nijeriya bayan 2023.

Saboda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yi wa jam’iyyar APC da Nijeriya shiri mai kyau.

Shugaban Majalisar ya ce Shugaba Buhari mutum ne da ba zai kakabawa ‘yan Nijeriya mutumin da ba sa kauna a zaben 2023 ba.

Shugaban Majalisar Jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdulllahi ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulkar Nijeriya har bayan shekarar 2023 saboda irin ayyukan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi a kasar nan.

Shugaban Majalisar ya fadi hakan ne a ranar Laraba 15 ga watan  Augusta a garinsu na Umaisha da ke karamar hukumar Toto a  jihar Nasarawa yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai.

Balarabe Abdullahi ya ce: “A lokacin da wa’adin mulkin Buhari za ya kare, ina tabbatar maka  cewa duk wanda zai biyo bayansa zai ci gaba da irin ayyukan da Buhari ke yi ne  saboda irin ingantattun ayyuka da yake yi wa kasa da jam’iyya.

“Ya ce za mu yi nazarin mutane bisa mizanin nagarta kuma duk wanda muka  amince zai iya maye gurbin Buhari, za mu mara masa baya.

“Saboda haka, ina tabbatar maka da cewa APC za ta ci gaba da mulkin Nijeriya har bayan 2023, babu shakka a hakan.”

Abdullahi ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su yi wa Buhari addu’a kuma su mara  gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule baya a yunkurinsu na magance  kalubalen tsaro da ake fuskanta a jihar da kasa baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!