Connect with us

LABARAI

Dakin Yunbu Ya Ruftawa Matashi, Ya Kashe Matarsa A Jigawa

Published

on

A shekaranjiya Lahadi ne wani mutum mai suna Musa Awaisu tare da matarsa Fadima Musa su ka gamu da iftila’in ruftawar daki a kansu a lokacin da su ke cikin wannan daki, inda har matar ta rasa ranta.

Wannan al’amari ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata a kauyen Auno da ke karamar hukumar Kafin Hausa a jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar ta Jigawa, SP Abdul Jinjiri, ne ya tabbatar wa da majiyarmu afkuwar wannan al’amari a yayin zantawarsu da wakilinmu.

SP Jinjiri ya bayyana cewa, wannan al’amari ya faru da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Lahadin da ta gabata a kauyen na Auno da ke karamar hukumar ta Kafin Hausa.

Haka kuma ya kara da cewa, mutumin mai shekaru ‎27 da haihuwa na tare da matarsa wadda ke da shekaru 20 sun gamu da wannan iftila’i a lokacin da su ke dakinsu wadda ya kasance ginin yunbu.

Ya ce, jim kadan bayan afkuwar al’amarin rundunar ‘yan sanda tare da agajin sauran al’umma makwabta su ka garzaya wannan waje domin ceto rayuwar wadannan bayin Allah.

Kakakin ya kara da cewa, duk da cewa rundunar tasu ta yi nasarar zakulo su daga cikin yunbun tare da garzayawa babban Asibitin daga karamar hukumar kafin Hausa, amma jim kadan bayan‎ zuwansu matar mai suna Fadimatu Musa ta rigamu gidan gaskiya.

Ya ce, zuwa yanzu dai tuni an gudanar da jana’zarta kamar yadda addinin Musulunchi ya tanada yadda shi kuma mijin, wato Musa Awaisu, wadda ke mawuyacin hali ke asibitin, ya na cigaba da karbar kulawar‎ likitoci.

Daga karshe kakakin ya yi kira ga al’umma da su kiyaye yanayin irin dakunan da su ke kwana, tare da addu’ar Allah ya gafarta mata shi kuma Allah ya ba shi lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: