Connect with us

KASUWANCI

Dalilin Buhari Na Shelar Kwace NEPA

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yi shelar cewar, tana duba yiwuwar sake kwato kamfanin rarraba wutar lantarkin na kasa da a ka fi sani da tsohon sunansa NEPA daga hannun yan kasuwa don ceto kasar na daga karancin wutar lantarki da takici tki cinyewa.

Matakin na Gwamnatin Tarayya da ke yunkurin dauka ya zo ne a daidai lokacin da za’a gudanar da cikakken nazari na karshe game da ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki watau DISCOS, don tabbatar da ko suna aikinsu yadda ya dace ba tare da kawo watacikas ba. Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya za ta biya yan kasuwan da suka mallaki kamfanonin rarraba wuta guda goma kudi har naira dala biliyan 2.4 a matsayin kudin fansa, daidai da naira biliyan 736.

An kuma ruwaito cewa, Ma’aikatar Ayyuka, Wutar Lantarki da Gidaje ta sanar da cewa, bayyana kamfanonin goma a matsayin wadanda ba zasu iya kawo cigaba a harkar wutar lantarki a kasar nan ba.

Idan za a tuna a watan a ranar 1 ga watan Nuwambar shekarar 2013 gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goolduck Ebele Jonathan ta sayar da hukumar wutar lantarkin kasarnanb ga wasu yan kasuwa bayan ra fasata gida uku, bangaren samar da wuta, bangaren dakon wuta da kuma bangaren rarraba wutar, amma har yanzu bangaren dakon wutar na hannun gwamnati ne.

Har ila yau, a satin da ya gabata ne, aka samu koma baya a adadin wutar lantarkin da kasar nan, inda kasarnan ta samu, daga megawatt 3,264 a ranar Litinin zuwa megawatt 2,842 a ranar Alhamis, wanda hakan ya kara jefa kasar nan a cikin mummunar karancin wutar lantarki.

Bugu da kari, Gwamnatin Tarayya ta zargi kamfanonin da kin samar da isashshen jari don amfani dashi wajen samar da wutar lantarki, inda hakan yajnyo garkame tashoshin wutar lantarki sha 17 cikin 27 saboda rashin sayan wutar da suke dashi a kasa.

Har ila yau, idan za’a tuna a watan Yulin shekarar 2015 ne Gwamnatin ta karbe kamfanin rarraba wutar lantarki na yankin jihar Yola, da ake kira da Yola Disco, sakamakon masu zuba hannun jari a kamfanin sun janye saboda matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas, amma har yanzu gwamnati bata biyasu kudinsu ba.

Mataki da Gwamnatin Tarayya take son dauka, ya zo ne a kan gaba, inda za’a gudanar da cikakken nazari na karshe game da ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki na DISCOS, don tabbatar da ko suna aikinsu yadda ya dace.

GwamnatinTarayya za ta biya yan kasuwan da suka mallaki kamfanonin rarraba wuta guda goma naira dala biliyan 2.4 a matsayin kudin fansa, kimanin naira biliyan 736 kenan

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: