Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamna Zamfara Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Jihar

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalen Maradun, ya aminta da nada Sabon Shugaban Ma’aikata jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe, sakamakon ritayar da tsohon shugaban, Alhaji Mujitaba Isah, ya yi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a takardar da Daraktansa na yada labarai Alhaji Yusuf  Idris da ya rabawa ‘yan Jaridu a  Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Gwamna Matawalen ya bayyana godiyarsa ga Tsohon shugaban akan yadda ya kawo wa Ma’aikatan jihar cigaba . kuma tsohon shugaban jajurtace ne wanda yayi aiki tukoru wajan kawo cigaba ga ma’aikatan jihar .gudunmuwar da ya bada bazata gushe ba a zukatan ma’aikata jihar .

Gwamna Matawale ya taya sabon shugaban Ma’aiakata Alhaji Kabiru Balarabe ,murnar zamowa shugaban Ma’aikatan jihar akan wannan dama da ya samu  . kuma yayi kira a gareshi da yayi aiki tukuru wajan ciyar da Ma’aikatan jihar gaba.

Sabon shugaban Ma’aikatan ,an haifeshi 15/3/ 1966 . ya kammala digirinsa a Jami’ar Usam Danfodiyo da ke Sokoto .ya fara aiki a ranar 21 /8/ 1991 ,a matsayin jami’i bincike  watau (Research Officer) a ofishin gwamnan mulki  Soja na jihar Sokoto ,inda har yakai matsayin mataimakin Babban Sakatare.

Alhaji Kabiru Balarabe ya rike mukamai da dama da Kwamitoci ,Wanda suka hada da  Sakataren tsohon shugaban kasa ,Alhaji Shehu Usman  Shagari  ,a shekara ta 1993 zuwa 1996 .sannan kuma ya wakilci jihar Sokoto a lokacin mulkin Soja na shugaban kasa Ibrahim Badanasi Babangida , a kwamitin mika mulki hannun farar hula a shekara ta 1992 zuwa 1993.

Alhaji Kabiru Balarabe shine farkon sakatare  watau ( pribate Secretary ) a jihar Zamfara a lokacin mulkin Kantoman Soja daga shekara ta 1997 zuwa 1999.

Kuma ya zamo sakataren dum – dum na mulkin fara hula na farko a jihar Zamfara ,a lokacin mulkin tsohon gwamna Ahmad Sani Yariman Bakura .kuma ya rike Kantoman tsohuwar karamar hukumar Kasuwar Daji.

Alhaji Kabiru Balarabe, zamuwar sa kwarare wajan tafiyar da mulki  da matakai da ban da ban yasan ya tsohuwar ministan Mata Hajiya Saudatu Bungudu ta dauke shi a matsayin mataimaki na musamman .kuma yanzu haka shine Babban Sakatare a Ofishin gwamnan jihar Zamfara

Kuma yanzu ya kure malejin mukaman  a fadin jihar Zamfara shine shugaban Ma’aikatan jihar Zamfara bakidaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!