Connect with us

KANNYWOOD

Kannywood: Yaushe Gwamnatin Kano Za Ta Farka?

Published

on

Makon da ya gabata na yi rubutu mai kama da bulaliya ga yadda harkokin finafinan Hausa ke tafiya musamman a Jihar Kano. Inda na bayanin yadda masana’antar ta faro da kuma matakan da Kano ta bi na yin uwa da makarbiya wajen juya masu gudanar da wannan sana’a ta finafinai don gudun kaucewa hanya.

Kwatsama, kwana daya da yin rubutun wani abu ya faru wanda yake neman zama silar tsagewar masana’antar gida biyu idan mahukunta ba su dauki mataki gaggawa tabbas hakan zai iya haifarwa al’ummar Hausawa babbar matsala, domin wadanda ba sa Hausawa za su iya amfani da wannan damar wajen shirya finafinai da Harshe, kuma su aikata abinda suke so. Matakin da wasu suka dauka da barranta kansu da masana’antar babbar barazana ce ga ita kanta gwamnatin Jihar Kano, domin za a samu karanci masu yin rajista da Hukumar Tace Finafinai, wanda hakan zai rage wa gwamnatin Kano kudaden shiga.

Duk mutumin da ya ke masana’antar fim ya san irin kalubale, matsaloli da wahalar da a ke sha. A shekarun baya, lokacin da a ke buga finafinai a kaset, manyan ‘yan kasuwa suna samun miliyoyin kudi, amma yanzu lamura sun canja, canki in canka kawa ake yi ta fuskar Kasuwanci. Wannan tasa da yawan masu shirya finafinan suka nemawa kansu mafita, watau yin waka su dora a YouTube da sauran kafafen sadarwar zamani. Ta haka suke shahara har manyan kamfanonin su dauke su domin yi musu talluka.

Mutane da yawan sun yi kokarin dora Kannywood kan turbar kwarai, amma rashin samun goyon bayan gwamnati ta fuskar samar da dandanlin cinikayya finafinai ya sa ana zaune kara zube, kowa yana yin abinda ya ga dama. A lokacin da duniya ta karbi sana’ar fim, idan ma Hausawan ba su yi ba, wasu za su kabilu za su ara harshen, su kuma yi amfani da Hausa ‘yan uwanmu wajen shirya fim kamar yadda muke gani yanzu.

Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau a shekarar 2003 ita za a ce ta fara fada sosai da masana’antar Kannywood baki daya, kasancewar sa gwamna da ake yi masa kallo mai tsattsauran ra’ayin addini. Mutumin da ya nada a zamanin sa domin jagorantar Hukuma Tace Finafina Da Dab’i, watau Abubakar Rabo, ‘yan fim na yi masa kallon matsangwami, wanda ya hana su rawar gaban hantsi. Ta bayyana karara irin rigingimu da bahallatsar da ta rika shiga tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin masana’antar. Wasu da dama hakan ya yi sanadiyar tafiyarsu gidan kaso, yayin da wasu ba shiri suka hijira daga Kano, cibiyar kasuwancin finafinai, suka koma wasu wuraren.

Babbar matsalar da Kannywood ta fuskanta ta bangaren bunkasar harkokin kasuwanci ya fara ne daga wannan lokacin, ta kai shirya fim din kan sa sai da ya gagari kowa, domin idan ka shirya ma babu kasuwar da za a kai. Hukumomin sun tarwatsa kowa a kokarinsu na saita al’amura. Maimaikon a yi gyara, sai lamarin ya koma barna. Maimakon janyo ‘yan fim din jiki, sai aka rika yi musu barazana da dauri, hakan ta sa wasu suka fice daga Kano, kuma ba su fasa shirya finafinan ba, wanda duk irin matakan tsaron da za a saka, sai finafinan sun shigo Kano ta barauniyar hanya, hukuma kuma ba ta da hurumin kama wani, tunda iya Kano kadai take aiki.

Allah ya albarkaci jihar Kano da abubuwa masu tarin yawa wadanda sauran jihohin suke kwaikwayo. Mutane da yawa sun bar garuruwan su na haihuwa suka dawo Kano da zama. Hakan a zahiri yana taimakawa kwarai wajen samawa ‘yan Najeriya ayyukan yi. Mutane da yawa sun samu miliyoyin naira, sun gina gidaje, sun zuba kudi a harkokin kasuwanci daban-daban, wanda haka ke taimakawa gwamnati matuka da gaske wajen rage mata nauyin dimbin matasa marasa ayyukan yi. Wannan dalili ya sa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya bawa masana’antar muhimmanci a mulkin karo na biyu. Ya kira ‘yan fim da suka yi gudun Hijira su dawo don ci gaban da harkokin su. Tsawon shekaru hudu na mulkinsa, harkar fim ta bunkasa, darajarta ta karu. Babu wani mutun da zai ci mutunci ‘yan fim ya zauna lafiya.

Shekarar 2015, sabuwar gwamnati karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa ‘yan fim tagomashin da babu gwamnatin da ta yi musu, inda ta dauki dan cikinta, ta bashi mukamin jagorancin Hukumar tace finafinan, lamarin da ya yi kama da namu ya samu. ‘Yan fim din sun yi farin ciki matuka da wannan ci gaba, kusan kowa ya rungumi tafiya da kuma tsari mai taken canji da sabon shugaban Hukumar ya bullo da shi. Kasuwar Kofar Wambai, wadda nan ne cibiyar hada-hadar finafinan Hausa, ta fara gamuwa da tasgaro a lokacin da masu sana’ar cajin waya suka gane tura fim a wayoyin hannu da kuma satar fasaha. An yi asara ta miliyoyin naira ta dalilin hakan. Duk da cewa hukuma ta yi kokarin dakile matsalar, amma a zahiri ta gaza, lamarin da ya sanya wasu hakura da sana’ar ta fim kwata-kwata. Masu taurin zuciya, su ne suka cigaba da jalautawa suna yin fim din, sannan su bi sahun masu satar fasaha domin kama su. Wannan ya janyowa ‘yan fim yin tafiye-tafiye zuwa garuruwa domin nemawa kansu mafita.

A irin wannan yanayi wasu ke yin hatsari a hanya su rasa ransu. Tuni babbar kasuwar Kofar Wambai ta mutu murus, kuma duk da haka hukuma ba ta fasa yi wa ‘yan fim barazana da dauri ba, domin wasu da yawa sun gamu da fushin hukuma da ya yi sanadiyar zuwan su gidan yari. Ko a makon da ya gabata, akwai Darakta Sunusi Oscar da Hukumar ta kama bisa zargin ya saki waka ba tare da an tantance ba.

A nawa nazari da ra’ayin, Kannywood ba tsangwana da barazana take bukata ba, illa tsari me kyau ta hanyar nuna soyayya da kauna. Yanzu ba lokaci ne na komawa tsarin shekarun baya – na kamu da dauri ba.

Muna 2019 yanzu, wanda saura wata hudu kacal mu shiga 2020. Duniya ta dade da karbar tsarin ci gaba fasahar zamani, amma Kannywood da masu ruwa da tsakinta sun gaza bullo da tsari wanda a shekaru daruruwa masu zuwa mutane za su amfana. Ko da yake, an samu bainar Manhajar Northflid da kuma irin kokarin da a yanzu haka mutane irin su Dakta Ahmad Sarari ke yi na samar da gidan talabijin na musamman da zai rika nuna finafinan Kannywood kadai. Tabbas irin wadannan labarai su ne labaran da Kannywood din ke bukatar ji da gani, ba batun dauri da kai mutane gidan yari ba.

Northflid Manhaja ce da aka kashe miliyoyin kudi wajen samar da ita ta yadda a yanzu ta zama madogara ta ci gaban kasuwancin finafinan Hausa, domin al’umma Hausawa mazauna kasashen wajen suna da damar kallon finafinan a duk lokacin da suke bukata. Kannywood TB kuwa da Ahmad Sarari ke kokarin samarwa. Da zarar ta fara aiki, dubun matasa da suka yi karatu a fannoni daban-daban na rayuwa za su iya aiki tare da ita, a hannu guda an ragewa gwamnati nauyin kula da ayyukan matasa.

Duk yadda muke kokarin wayar da kan al’umma wajen bin doka, amma dauri da kaiwa gidan yari ba shi ne mafita ga mutanen da suke sana’a ba. Tallafi suke bukata na bunkasa masana’antarsu a daidai wannan lokaci. Gudunmawa suke bukata daga wurin hukumomi ta kowane yanayi. Idan har wasu na waje na yunkurin shigowa su zuba hannun jari, irin wadannan kalamai za su razana su, su koma wani bangaren don zuba kudadensu.

Misali, mu kalli jihohin Borno da Zamfara, gwamnati kokari take na fito da mutane daga gidan yari, tana koya musu sana’o’i domin su dawo rayuwa cikin mutane, duk da cewa sun aikata manyan laifuka na tada hankali da kisan jama’a. Wannan zai nuna mana cewar ita gwamnati a koda yaushe, ba wai dauri da kamun take so ba, ta fiso mutane su rayu cikin yarda da aminci. Ashe kenan, kamu da dauri ba shi ke ganin matsala ba, janyo mutane jiki a mu’amalance su shi ne mafita.

Kannywood dai masana’anta ce da ta samun gindin zama ba Arewa kadai ba, Najeriya baki daya. Idan Hausawa suka daina yin fim, to tabbas Yarbawa da sauran manyan kabilun Najeriya za su karbi sana’ar su rika yi, ta yadda al’ummarmu ba za su iya hana su yin abinda suka ga dama ba.

Matsalar Kannywood guda daya ce a yanzu, Kasuwanci, gwamnati ta yi tsari, ta duba yiwuwar tallafawa masana’antar da a lokacin zabuka ke bawa ‘yan siyasa gudunmawa idan za a ce kamfen. Maganar kamu da daure mutane ba za ta haifar Kano da gwamnatin Kano da mau ido ba, domin daga lokacin da wasu suka balle tabbas shawo kansu zai yi matukar wahala. Ba koda yaushe ne barazana da kokarin daure mutane ke maganin matsala ba, ana bukatar tsarin diflomasiyya wajen gudanar da wasu abubuwan.

Har ila yau, wadannan matasan da suke yin wakoki suna dorawa a YouTube ba haka kawai suke yi ba, akwai dalili. Kamata ya yi hukuma ta zauna, ta kalli matsalar daga tushe, kan menene yake haifar da ita. Idan kuma tana bukatar gudunmawa, a shirye na ke.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: