Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Matakin Kara Haraji Ya Kara Iyuwar Tabarbarewar Tattalin Arzikin Amurka

Published

on

An lura a kwanakin baya cewa, ribar takardun lamunin Amurka na tsawon shekaru biyu ta fi na tsawon shekaru goma yawa, wannan ya sanya kasuwar takardun lamunin kasar shiga cikin hadari, a don haka masu zuba jari sun yi hasashen cewa, tattalin arzikin Amurka zai gamu da hadarin tabarbarewa.
Kan wannan, mashawartan fadar White House suka rika bayyana a wani shirin gidan talibijin daya bayan daya jiya Lahadi 18 ga wata, inda suka musunta cewa, babu alamar dake nuna tabarbarewar tattalin arziki a kasar ta Amurka, amma sabbin alkaluman tattalin arzikin da aka fitar da ra’ayin al’ummun Amurka na yin adawa da matakin kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin da gwamnatin Amurka ta dauka sun shaida cewa, matakin kara haraji ya tsananta hadarin tabarbarewar tattalin arziki a kasar ta Amurka.

Hakika ribar takardun lamuni za ta rika karuwa, idan ribar takardun lamuni na tsawon lokaci ba ta kai ta takardun lamuni na gajeren lokaci ba, to lamarin ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar zai gamu da hadarin tabarbarewa a cikin watanni sha biyu masu zuwa. A cikin shekaru 50 da suka gabata, Amurka ta sha gamuwa da irin wannan matsala kafin ta gamu da rikicin tabarbarewar tattalin arziki. Yanzu haka musamman ma a ranar 14 ga wata, shi ne karo na farko tun bayan shekarar 2007, ribar takardun lamunin Amurka na tsawon shekaru biyu ta fi na tsawon shekaru goma yawa, masu zuba jari sun damu matuka, har alkaluman kasuwar hanayen jari na kasar sun ragu da kusan kaso 3 bisa dari.

Jagoran kamfanin samar da wutar lantarki na Amurka Nicolas Akins ya bayyana cewa, ya ga alamar tabarbarewar tattalin arziki, kamar yadda aka fuskanta a baya, jagoran kamfanin ba da shawara na Richard Bernstein ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin Amurka zai fuskanci tafiyar hawainiya, kuma saurin karuwar tattalin arzikin kasar zai ragu fiye da hasashen da aka yi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: