Connect with us

LABARAI

Muna Samun Cigaba A Kasuwar Gwarin Kasa Da Kasa Ta Mile 12 – Abdullahi Zarewa

Published

on

Wani matashin dan kasuwar sayar da kayan gwari a jihar legas mai suna Alhaji Abdullahi Zarewa dake karamar hukumar rogo ta jahar Kano, kuma jamiin hulda da jama’a a akasuwar wanda yake gudanar da harkokin kasuwancinsa a babbar kasuwar mile 12 intanashinal maket a jahar legas, ya bayyana cewa babbar kasuwar ta sayar da kayan gwari a Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Sampam Dallatun Abeokuta ya bayyan cewe babbar kasuwar ta sayar da kayan gwari a Najeriya tana kara samun cigaba ta fannin  kasuwancin gwari da sauran al-amuran da suka shafi reyuwar al-ummar kasuwar a duk fadin jihar legas.

Jami’in hulda da jama’a na kasuwar yayi wannan tsokacine a zarewa ta jahar kano jim kadan bayan kammala daurin auren yarsa mai suna  Aishatu da angonta Buhari wanda ya gudana a garin zarewa a ranar asabar din da ta gabata, kuma yake nuna farin cikinsa a gameda yanda yaga tururuwar al-umman hausawa ma zauna jahar legas da kano domin zowa tayashi murnar tare da shaidawa idansu yanda daurin auren zai gudana a garin zarewa, sannan kuma ya samu halartar shugaban kasuwar ta mile 12 Alhaji Shehu Usman Sampam tareda yan majalisansa, ya kara da cewar babu shakka kasuwar ta yan gwari tana kara samun cigaba a wajan kasuwancin gwari da zaman lafiyar al-umma da sauran makamantansu inji shi da fatan Allah yaci gaba masa da jagoranci amin.

Sannan ya shawarci  al-ummar kasuwar dasu cigaba da bawa shugaban kasuwar hadin kai da goyon baya bisa ga kokarinsan na ciyar da kasuwar gaba da al-ummar cikinta baki daya, sannan yaci gaba da kira ga shuwagabannin bangarorin kasuwar da suci gaba da hada kai da goyan baya a wajen gudanarda aiyukan cigaban kasuwar dana al-umma baki daya, acewarsa da fatan Allah ya cigaba da yimasa jagoranci a wajen al’amuran da suka shafi kasuwar dana al-ummar kasuwar bakida.

Sannan yaci gaba da cewa yana mai isar da sakon godiya da fatan alheri ga dumbin jama’ar da suka zo zarewa domin tayashi murnar daurin auren yarsa Aishatu da angonta Buhari injishi da fatan kowa ya koma gida lafiya, acewarsa godiya ta musamman ga al-ummar da suka fito daga sassa da ban daban domin tayashi wannan murnar daurin aure injishi musamman shugaban kasuwar ta mile 12 Alhaji Shehu Usman Sampam da yanmajalisarsa na kasuwar ta mile 12 da iyayen kasuwar kamar haka: Shugaban dattawan kasuwar Alhaji Isah Muhammed da tsohon shugaban kasuwar Alhaji Haruna  Muhammed da Alhaji Habu Paki garkuwan paki da Alhaji Abdulwahabu tsoho babangida da Alhaji Abdullahi burama da tsohon sakataren kasuwar ta mile 12 Alhaji wada yaro kiru da sauran jama’a da yawa wanda babu lokacin cigaba da kiran sunayensu injishi da fatan kowa ya koma masaukinsansa lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!