Connect with us

LABARAI

‘Yan Sanda Sun Tsinto Gawar Macen Da Aka Yasar A Kwalbati

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai, sun tsinci gawar wata mace tsirara yashe cikin kwalbati a yankin Nyiman Layout da ke Makurdi a jiya Litinin.

Majiyarmu ta nakalto cewar macen wacce har zuwa yanzu ba a kai ga tantance wacece ita ba; an iya gano cewar an kasheta ne biyo bayan fyade da aka mata kana aka jefar da ita a kwalbati da ke gaban cocin Pentecostal da ke yankin.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar DSP Catherine Anene ya tabbatar da cewar sun tsinto gangan jikin mamaciyar da sanyin safiyar ranar Litinin, yana mai karawa da cewar za su ci gaba da zafafa bincike domin gano hakikanin musabbin zancen.

Anene ya ce ‘yan sanda ba za su ce komai a daidai wannan lokacin ba domin a cewarsu suna kan kokarin gano wanda tsautsayin ya sameta da tabbatar da wacece ita.

Jami’in ya kara da cewa, tunin suka kai gawar zuwa dakin adana gawarwaki a cikin asibiti.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: