Connect with us

MANYAN LABARAI

Ambaliya A Jigawa:Mutum Shida Sun Halaka, Gidaje Dubu Sun Rushe

Published

on

Kimanin mutane shida ne a ka tabbatar da rasuwarsu tare da rugujewar gidaje sama da dubu a wasu kanana hukumomi a jihar Jigawa.

Wannan ‎al’amari ya afku ne sakamakon barkewar ruwan sama kamar da bakin kwarya cikin kwanaki hudun da suka gabata.

Al’amarin wadda ya fi tsamari a kananan hukumomin Guri, Kiri-Kasamma, Kafin Hausa, Dutse, Birnin Kudu da wasu yankunan masarautar Hadeja, ya kuma yi awon gaba da amfanin gona wadda yawansa bazai kididdigu ba.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa, Alhaji Sani Yusuf Babura, ne ya tabbatar da afkuwar wannan al’amari a jiya lokacin da ya jagoranci tawagar mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Umar Namadi, domin kewayawa tare da yin jaje ga wadanda wannan iftila’i ya shafa.

‎Sannan ya bayyana cewa, cikin wadanda su ka rasa rayuwarsu akwai wata mata mai dauke da juna biyu gami da sauran yara kanana, baya ga raunata wadansu wadda a halin yanzu su ke kwance a asibiti don karbar magani.

Babura ya zayyana sunan matar mai juna biyu da Halimatu Manu tare da yaranta guda biyu A’isha Manu mai shekaru hudu da kuma kanenta Dauda Manu wadda shi kuma ya ke da shekaru biyu da haihuwa.

Haka kuma ya ce, sun rasu ne sakamakon ruftawar daki akansu a daidai lokacin da a ke tsala ruwan samar kamar da bakin kwarya a yammacin jiya litinin wadda ya dauki dogon lokaci kafin tsayawarsa.

Shugaban kuma kara da cewa bayan wadannan, hukumar tasu kuma ta sami rahoton rasuwar wasu ma’aurata biyu mata da miji wadda su ma su ka rasu a kauyen Madaci dake karamar hukumar Kiri-Kasamma sakamakon ruftawar dakin yunbu a kansu.

Sannan kuma yace a ranar lahadin data gabata‎ iftila’in ya fadawa wasu mata da mijin masu suna Musa Awaisu da Fadimatu Musa a karamar hukumar Kafin hausa yadda matar ta rasu shi kuma mijin ya sami munanan raunuka wadda a yanzu haka ke Asibiti na karbar magani.

Wakilinmu ya zagaya wasu wuraren da wannan al’amari ya shafa yadda ya ganewa idanunsa yadda gidaje, gadoji da amfanin gona masu tarin yawa suka lalace sakamakon wannan ambaliya.

Shi kuwa da ya ke zagayen jajentawa wadanda al’amarin ya shafa, mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi ya jajenta iyalan wadanda ‎suka rasa rayukansu tareda addu’ar Allah ya baiwa wadanda suka yi raunuka lafiya.

Sannan ya sha alwashin cewa gwamnatin za ta tallafawa wadanda al’amarin ya shafa domin rage musu radadin asarar da suka tafka sakamakon wannan ambaliya.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnatoci da sauran kungiyoyin bada tallafi na duniya da su kawowa al’‎ummar wannan jiha dauki domin rage radadin wannan iftila’i da ya same su.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: