Connect with us

LABARAI

Kashifu Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NITDA

Published

on

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta nada Kashifu Abdullahi a matsayin sabon Daraktan hukumar lura da ci gaba bangaren sadarwa da kimiyya wato NITDA.

Hadiza Umar, shugaban sashen hulda da jama’a na NITDA ita ce ta tabbatar da nadin na sag a manema labarai a Abuja. Hadiza Umar, ta ce; wata sanarwa da Kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fitar ita ta tabbatar da nadin sabon Darakta Janaral din.

Rahotanni sun tabbatar da cewa; an nada Kashifu ne sakamakon zaban Dk. Isa Pantami a matsayin Minista da shugaban kasa Buhari ya yi.

Kafin nadin Abdullahi ya rike mukamin PO na CBN kuma shi ne na biyu a NITDA a matsayin Technical Assistant ga Pantami.

An haifi Abdullahi a ranar 21 ga watan Fabarairun 1980. Ya kammala Digirinsa na farko a bangaren Kwamfuta daga Jami’ar ATBU. Yanzu haka shi ne Darktan NITDA na biyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!