Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kebbi: ‘Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Sa-kai Bisa Kashe Masu Garkuwa

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Kebbi, ta cafke ‘yan kungiyar sa-kai guda shida, bisa zargin su da kashe wasu wadanda a ke kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne. Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Mista Garba Danjuma, shi ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Talata a Birnin Kebbi. Danjuma ya bayyana cewa, ‘yan kungiyar sa-kai daga kauyen Kanji cikin gundumar Mahuta da ke karamar hukumar Fakai ta jihar, sun damke wani mutum biyu masu suna Muhammad Dankarami da kuma Muhammadu Buda wadanda a ke zargin masugarkuwa da mutane ne a yankin Maidangwami.

Ya kara da cewa, ‘yan kungiyar sa-kan ba su bai wa wadanda a ke zargin damar yi musu bayani ba, inda su ka kashe su har lahira a nan take tare da banka wa gawarwakinsu wuta. A cewarsa, an samu nasararcafke ‘yan kungiyar sa-kai bisa aikata wannan mummunan lamari. Danjuma ya ce, “idan za ku amince da ni, doka ba ta bayar da damar kashe wanda a ke zargi ba tare da kone gawarsu. Wannan mummunan hukunci ne, kuma ba a taba lamintar irin wannan hukunci a kasar nan ba”.

Ya bukaci mutane su hada hannu da karfe wajen yakar muyagun laifuka. Ya kara da cewa, “za mu cigaba da hada kai domin dakile ayyukan ta’addanci a cikin wannan jihad a kuma Nijeriya gaba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!