Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Legas: ‘Yan Sanda Sun Damke Masu Aikata Miyagun Laifuka Da Kwato Makamai

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legas, ta samu nasarar damke wani dan kungiyar asirin mai suna Biodun Adelokun. Haka kuma rundunar ta samu nasarar cafke ‘yan kungiyar asirin guda 32 tare da kwato muyagun makamai a cikin wannan mako. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, DSO Bala Elkana, shi ya tabbatar da wannan kamen a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa, an samu nasarar damke wani kasurgumin dan kungiyar asiri mai shekaru 32, shi dai wannan kasurgumin dan kungiyar asiri, mamba ne a kungiyar asiri ta Aiye Confraternity, kuma an cafke shi ne a ranar Asabar.

Elkana ya kara da cewa, rundunar ‘yan sanda masu yaki da ayyukan kungiyar asiri ne su ka samu nasarar damke wanda a ke zargi, lokacin da su ke gudanar da sintiri a kan titin Mosafejo da ke cikin yankin Ajegunle, an dai cafke shi ne da wata karamar bindiga kirar gida. Ya ce, wanda a ke zargi ya bayyana cewa, lallai kungiyarsa ce ta ke da alhakkin rikece-rikecen ta’addanci  wanda ya afku a yankin Ajegunle. “Ana gudanar da binciken a kan lamarin, sannan ya na kokarin yadda za a samu nasarar cafke sauran ‘yan kungiyarsa wadanda su ka gudu. Za a gurfanar da wadanda a ke zargi a kotu idan a ka kammala bincike,” in ji Elkana.

A wannan rana, tawagar ‘yan sanda da ke sashe na takwas a yankin Ogudu, sun kai samame a maboyar ‘yan kungiyar asiri a yankin Bariga. A wannan samame an samu nasarar damke shugaban ‘yan kungiyar asiri mai shekaru 39, a gidansa da ke kan titin Kajora cikin yankin Bariga, an dai cafke shi ne tare da wasu ‘yan kungiyar asirinsu guda 22. “Sun bayyana cewa, su ne su ke da alhakkikin kashe-kashe da kuma ayyukan ta’addanci a yankin Bariga. “Ana gudanar da bincike a kan lamarin, sannan idan a ka kammala za a gurfanar da wadanda a ke zargi a gaban kuliya,” in ji.

Ya cigaba da cewa, a samamen da rundunar ‘yan sanda na yankin Bariga su ka kaddamar a ranar Talata, a kan titin Oyenaya cikin yankin Bariga, ya yi sanadiyyar cafke wani dan kungiyar asiri mai shekaru 20 tare da wasu mutum biyar ‘yar kungiyarsa. Elkana ya ce, an damke wasu mutum biyu wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne ranar 24 ga watan Yuli, a yankin Itabale Igbolomu da ke cikin garin Owutu ta Ikorodu, a lokacin wani musayar wuta. Ya ce, an samu nasarar kwato karamar bindiga kirar gida daga hannunsu. Ya dai bayyana cewa, nan bada jimawa ba za a gurfanar da dukkan wadanda a ke zargi a gaban kotu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!