Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Neja: ‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Fashi Da Makami Hudu

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Neja, ta samu nasarar cafke mutum hudu wadanda a ke zargi da fashi da makami, wadanda su ke yi wa masu motoci tare da mazauna yankin Kanaba kusa da karamar hukumar Mokwa ta Jihar fashi. Wadanda a ke zargin dai su ne Garba Mande, Mohammed Mande, Ahmadu Mande da kuma Mohammed Awwali, an bayyana cewa su na gudanar da wannan mummunar aika-aikan ne daga sassanin Funali da ke Mokwa.

An bayyana cewa, ‘yan sanda sun samu nasarar cafke su ne a Tashan Hajiya lokacin da su ke yi wa mutanen yankin fashi.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, wadanda a ke zargin sun yi wa wata mata mai sayar da abinci fashi kafin a samu nasarar cafke su.

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar, Muhammad Abubakar, ya tabbatar da cafke wadanda a ke zargi. Ya bayyana cewa, sun yi wa wata mata mai suna Bose Adeyemi daga Jihar Ogun fashi lokacin da ta ke kokarin tafiya zuwa Jihar Bauchi daga garin Mokwa. A cewarsa, tawagar ‘yan bindigar rike da bindigogi da kuma sanduna sun tsaida motoci tare da wasu mutane, inda su ka yi musu fashi tare da amsar kudi har naira 93,000 da kuma wayar salula na Adeyemi.

Abubakar ya kuma kara da cewa, ‘yan sanda sun kwato bindiga guda daya, adduna guda biyu da kuma wayar salula guda biyu daga hannun wadanda a ke zargin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!