Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sharhi: Da Gaske Ne Twitter Da Facebook Ba Sa Jin Kunya?

Published

on

Kwanan nan, shafukan sada samunta na Twitter da Facebook na kasar Amurka sun sanar da toshe wasu asusu masu mu’amala da su kusan dubu, bisa dalilin wai sun watsa labaran karya dangane da zanga-zangar da aka gudanar a Hong Kong, wadanda kuma suka samu goyon baya daga gwamnatin kasar Sin.

Idan an yi la’akari da sanarwar, za a gane cewa asusun da aka toshe sun kasu gida biyu, na farko su ne wadanda suka bayyana rashin amincewarsu da yadda aka gudanar da ayyukan nuna karfin tuwo da suka hada da kai hari majalisar dokokin Hong Kong da ma ‘yan sanda, da hana zirga-zirgar bas bas da kuma dukan ‘yan jarida, na biyu kuma su ne wadanda suka bayyana goyon bayansu ga matakan da ‘yan sandan Hong Kong suka dauka kan masu nuna karfin tuwo. Sai dai Twitter da Facebook sun dauki wadannan labaran da suka bayyana ainihin gaskiyar abubuwan da ke faruwa a Hong Kong a matsayin labaran karya.

Me Twitter da Facebook za su ce game da maganar ‘yancin fadin albarkacin baki kan yadda suka gurbata gaskiyar lamarin, kuma da gaske ne ba su jin kunya?

 

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: